Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta shigar da kara kotu tana tuhumar tsohon Ministan Shari’a na kasar Abubakar Malami SAN da dansa Abubakar Abdulaziz Malami da laifuka 16 da suka shafi almundahanar kudi har Naira biliyan 1.014.
An bayyana cewa daga cikin wadanda ake tuhuma tare da tsohon ministan da ɗansa har da wata mata Hajia Bashir Asabe.
A bayanan tuhumar, gwamnati tana zargin Malami, ɗansa, da karin wasu mutanen da hannu a satar kuɗi da ɓoye su da suka kai Naira biliyan 1,014,848,500.00) da ake zargin an gano su a wani bankin kasuwanci.
A tuhume-tuhume 16 da aka gabatar, gwamnatin Nijeriya ta yi zargin cewa tsakanin watan Yulin 2022 da Yunin 2025, a Abuja da kuma bisa ikon kotu, waɗanda ake tuhuma sun sayi Kamfanin Metropolitan Auto Tech Limited don ɓoye haramtaccen wajen da aka samo kudaden.
Tuhumar ta kuma yi zargi, a wani ɓangare, cewa waɗanda ake tuhumar sun yi amfani da kamfanin a matsayin wani ɓangare na ɓoye asalin inda kudin suka fito da kuma motsinsu daga nan zuwa can, lamarin da gwamnati ta ce ya zama satar kudade a karkashin dokokin Nijeriya.
An ce laifin da ake zargin ya saba wa Sashe na 21(c) na Dokar Hana Satar Kuɗi ta 2022, kuma za a iya hukunta mai laifin a ƙarƙashin Sashe na 18(3) na wannan Dokar.
Tuhume-tuhumen 16 sun bayyana yadda ake zargin Malami da hannu a badakalar kudin haram. ta hanyar amfani da kamfanin Metropolitan Auto Tech Limited.
Malami ya yi aiki a matsayin Babban Lauya kuma Ministan Shari'a na Nijeriya daga 2015 zuwa 2023 a karkashin gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.















