| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Maroko ta fitar da takardun kudi da sulalla na bikin AFCON
Babban bankin Maroko, Bank Al-Maghrib ya ce kuɗaɗen suna da tambarin Maroko da alamomin ƙwallon ƙafa kamar sabbin filayen wasan da aka gina.
Maroko ta fitar da takardun kudi da sulalla na bikin AFCON
Takardar kuɗi na tunawa da AFCON wanda Bank Al-Maghrib (BAM) ya bayar. / Others
23 Disamba 2025

Maroko ta fitar da takardar kuɗi da sulalla don murnar bikin Gasar Ƙasashen Afirka ta AFCON 2025, don tunawa da kasancewar ƙasar mai masaukin wannan gasar da ke gudana a halin yanzu.

Kuɗaɗen sun ƙunshi alamomin ƙasa tare da isharorin ƙwallon ƙafa da sabbin cibiyoyin wasanni da aka samar, in ji babban bankin ƙasar, Bank Al-Maghrib (BAM).

A cikin wata sanarwa, bankin ya ce ya saki sulen azurfa mai daraja a fuska ta dirhami 250 (daidai da dalar Amurka $27.5), da takardar kuɗi mai darajar dirhami 100.

“Dukkan matakai na zayyana da aikin ƙera wannan sulalla da takardun kuɗi, ƙwararru 'yan Maroko ne suka yi su,” in ji bankin.

Kuɗaɗen na tunawa da gasar an yi su ne da azurfa da haɗaɗɗen tagulla, kuma suna da nauyin kusan giram 30. Fuskarsu na ɗauke da hoton Sarki Mohammed VI, tare da rubuce-rubucen 'Mohammed VI' da 'Royaume du Maroc' cikin Larabci.

An ayyana shekarar fitarwa a matsayin 1447-2025, wanda kuma aka rubuta da haruffan Larabci da na Tifinagh.

Bankin na BAM ya ce takardun kuɗin dirhami 100 suna nuna yadda Daular ke ɗaukar wasanni, da muhimmanci kuma suna haskaka sabbin kayayyakin wasanni da aka gina.

An fitar da kuɗaɗen ne na taƙaitattun adadi a ranar Litinin, kuma za su yi yawo tare da takardun dirhami 100 na yau-da-kullum.

A gaban takardar akwai hoton Sarki Mohammed VI, tambarin ƙasa, hoton Cibiyar Wasanni ta yarima Moulay Abdellah da ke Rabat, taswirar Afirka, zanen Maroko da kuma ƙwallo.

Maroko tana ɗaukar nauyin gasar AFCON karo na 35, wadda aka fara ranar Lahadi 21 ga Disamba inda za a buga wasanni a birane da dama a cikin ƙasar.