Da fari, a minti na 36 ne dan wasan Super Eagles Semi Ajayi ya jefa kwallo a ragar Taifa Stars wand aya sanya Nijeriya zama a kan gaba.
Haka aka ci gaba da fafatawa har zuwa karshen zagayen farko na wasan.
Bayan na dawo zagaye na biyu, dan wasan Taifa Stars Charles M’Mombwa ya zura kwallo a ragar Nijeriya wanda ya sanya wasan koma wa sabo, 1 da 1.
Amma cikin hanzari, kasa da mintuna biyu da Tanzania ta farke kwallonta, dan wasan Nijeriya Ademola Lookman ya jefa kwallo ta biyu a ragar Tanzania.
An tashi wasan Nijeriya na da kwallaye biyu, Tanzania kuma na da kwallo daya tilo.
Kungiyar Super Eagles ce ta mamaye zagayen farko na wasan, inda Akor Adams da Victor osimhen suka yi ta kai farmaki.
A rukunin C na gasar ta AFCON 2025 da ake buga wa a kasar Morocco, akwai kasashen Nijeriya, Tunisia, Tanzania da Uganda.











