Yadda bijire wa magunguna ke sake taɓarɓarar da ƙoƙarin kawar da cutar malaria a Afirka
AFIRKA
5 minti karatu
Yadda bijire wa magunguna ke sake taɓarɓarar da ƙoƙarin kawar da cutar malaria a AfirkaHukumomin kiwon lafiya suna ta rarraba wannan sabon abin kariya, wanda ya haɗa maganin kashe kwari na pyrethroid da wani sinadari na biyu kamar chlorfenapyr ko pyriproxyfen, a cikin sassa na Afirka masu fama da yawan maleriya.
Yadda bijire wa magunguna ke sake taɓarɓarar da ƙoƙarin kawar da cutar malaria a Afirka / Reuters
kwana ɗaya baya

A karon farko cikin shekaru, 'ya'yan Amina Lawal sun yi barci cikin aminci ba tare da kamuwa da rashin lafiya ba duk da marka-markar ruwan sama.

Amina mai shekaru 32 uwar 'ya'ya uku a arewacin Nijeriya tana godiya ga gidan sauron da ta samu bara, mai ruɓi biyu da kuma sinadaran magani a jikinsa, wanda yana cikin sabbin kayayyakin matakan kariya daga maleriya da ake rabawa a yankin.

'Kowace damina sai mun shiga fargabar yin rashin lafiya saboda azabar sauro,' Amina ta shaida wa TRT Afrika. 'Sabon gidan sauron da kuma allurar rigakafin maleriya da aka yi wa 'ya'yana a asibiti yanzu sun taimaka mana sosai. Muna barci cikin kwanciyar hankali.'

Hukumomin kiwon lafiya suna ta rarraba wannan sabon abin kariya, wanda ya haɗa maganin kashe kwari na pyrethroid da wani sinadari na biyu kamar chlorfenapyr ko pyriproxyfen, a cikin sassa na Afirka masu fama da yawan maleriya.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta lura a cikin rahotonta na shekara-shekara kan maleriya cewa sabbin kayan kamar gidan sauro mai sinadaran kariya da kuma alluran rigakafin maleriya da ake ba da shawara a yi sun taimaka wajen mutum miliyan 170 kamuwa da maleriya a bisa ƙiyasi da kuma hana mutuwar fiye da mutum miliyan ɗaya a shekarar 2014 kawai.

Tun daga 2021, kimanin kasashe 24 ne suka saka allurar rigakafin maleriya a cikin shirye-shiryen rigakafin yara.

Rigakafin maleriya na yanayi (Seasonal malaria chemoprevention), wata hanya da yara a yankunan da cutar ta fi yawa kamar Sahel ke karɓar magungunan rigakafi na wata-wata, ta taimaka wajen kare yara miliyan 54 a kowace shekara a cikin kasashe 20.

A shekarar 2012, adadin yaran da suka amfana da wannan kusan 200,000 ne.

Wasu ƙasashe sun riga sun kawar da maleriya yayin da wasu ke cikin kusantar samun nasarar.

WHO ta tabbatar da cewa Cabo Verde da Misira sun kawar da cutar maleriya a 2024.

Georgia, Suriname da Timor-Leste suka shiga jerin wannan shekara, wanda ya ɗaga adadin zuwa ƙasashe 47 da yanki guda.

Abin damuwa

Duk da alamun ƙarfin zuciya, wasu sassan nahiyar na bayar da rahoto kan abin da ma'aikacin lafiya na al'umma John Mwangi ya kira 'canji mai tayar da hankali' a sassauyawar maleriya.

'Magunguna ba sa aiki kamar da,' in ji Mwangi, wanda ke aiki a tsaunukan yammacin Kenya, ga TRT Afrika.

'Muna samun yara suna shigowa suna karɓar maganin kamar yadda aka saba, amma zazzabi yana ci gaba. Haka kuma yana ɗaukar lokaci mai tsawo kafin su farfado.

Kamar dai da cutar da ƙwayoyinta duk suna sassauya ne. Muna wata gaɓa da fafutukar daƙile cutar ta ƙaru.

Abin da Mwangi ya lura da shi ya nuna babbar damuwar da ke cikin rahoton wannan shekara. Duk da tasirin sabbin matakan kariya, an kiyasta cewa amutum miliyan 282 ne suka kamu da maleriya sannan mutum 610,000 a 2024, wanda ya haura na shekarar da ta gabata da miliyan tara.

Kashi 95% na waɗannan mace-mace sanadin maleriya a afirka suke faruwa, kuma mafi yawansu yara ne ƙasa da shekaru biyar.

Abin da ya fi ɗaga hankali shi ne yadda ginshikin samar da maganin maleriya yake fuskantar barazana.

WHO ta ruwaito cewa ƙaruwar juriya ga magungunan maleriya, musamman waɗanda ke da alaƙa da artemisinin, yanzu an tabbatar da shi ko ana zargin yana faruwa a aƙalla ƙasashe takwas na Afirka.

'Sabbin matakan hana maleriya suna ba mu sabon fata, amma har yanzu muna fuskantar manyan ƙalubale,' in ji daraktan janar na WHO, Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus.

Ya kuma yi gargaɗi cewa karuwar lamura, juriya ga magunguna, da rage tallafi na iya mayar da hannun agogo baya kan ci gaban da aka samu a cikin shekaru 20.

Baya ga juriya ga magunguna, gwaje-gwajen gano maleriya cikin gaggawa suna zama marasa tabbas saboda sauye-sauye a ƙwayoyin cutar. Haka nan yanzu sauron bai faye jin maganin kashe shi ba.

Anopheles stephensi, wani nau'in sauro mai juriya, yanzu shi ne babban sanadin maleriya a ƙasashe tara na nahiyar.

Al'amuran yanayi masu tsanani da rikici suna ƙara haɗari: ɗaya yana ƙara yawaitar barkewar cuta, ɗayan kuma yana raunana tsarin kiwon lafiya.

Karancin Kuɗi

A faɗin duniya duka, an kashe dalar Amurka 3.9 biliyan wajen daƙile maleriya a 2024, amma hakan bai kai rabi na burin dalar Amurka 9.3 biliyan ba.

'Rahoton Duniya kan Maleriya ya nuna cewa juriya ga magunguna na ƙaruwa. Martaninmu dole ya zama mai ƙarfi haka ma,' in ji Dr Martin Fitchet na ƙungiyar bincike ta Medicines for Malaria Venture.

Ya nuna ci gaban maganin haɗin farko wanda ba ya amfani da artemisinin a matsayin farkon babi na sabon tsarin juriyar maleriya.

Hanyar da za a bi gaba, kamar yadda rahoton WHO ya bayyana, tana buƙatar ƙarfafa amsa mai 'ƙasa ke jagoranta, abokan haɗin gwiwa na tallafawa' wadda ta dogara ga mayar da ƙudurin siyasa kamar na Sanarwar Yaoundé zuwa aiki da albarkatu.

Yaki ya mai da hankali wajen faɗaɗa rabon kayan ceton rai waɗanda ke aiki yayin da ake ƙirƙira gaba ɗaya don wuce juriya ga magunguna da sinadaran kashe kwari.

Ga Amina a Nijeriya, sabbin kayan kariya daga maleriya suna nufin barci mai salama. Ga John a Kenya kuwa, suna nuna raguwar fata har sai an turo ƙarin taimako.

Miliyoyin rayukan da aka ceta a bara suna tabbatar da cewa akwai yiwuwar a kawar da maleriya.

'A ƙarshe mun samu garkuwa,' Amina ta faɗa wa TRT Afrika. 'Muna addu'a ka da wannan kariya ta gaza.'