| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Courtois ba zai buga wasan Real Madrid da Olympiacos ba
Real Madrid ta tabbatar da jinyar golanta, Thibaut Courtois, da kuma ɗan wasan baya, Dean Huijsen a wasansu da Olympiacos na gasar Zakarun Turai a makon nan.
Courtois ba zai buga wasan Real Madrid da Olympiacos ba
Courtois na da shekaru 33 a duniya, kuma shi ne babban golan Real Madrid a halin yanzu.
25 Nuwamba 2025

A Laraba 26 ga Nuwamba ne Real Madrid za ta kece raini da Olympiacos a cigaba da Gasar Zakarun Turai ta UEFA, inda za ta je wasan ba tare da manyan ‘yan wasanta biyu ba.

Babban golan Madrid, Thibaut Courtois da kuma ɗanwasan baya, Dean Huijsen suna jinyar da za ta hana su buga wasan mai muhimmanci.

Mai shekaru 33, Courtois na fama da ciwon ciki na Gastroenteritis, bayan likitocin ƙungiyar sun duba lafiyarsa.

A yanzu dai za a ci gaba da saka ido kan murmurewar mai tsaron gidan, a cewar wata sanarwa ndaga ƙungiyar ranar Talata.

Rahotanni daga Madrid na cewa Courtois bai halarci wasan atisaye da tawagar ba, kuma akwai shakku kan warkewarsa kafin wasansu na ƙarshen mako da Girona a gasar La Liga.

Fagen sa’a

A wasan Zakarun Turai na mako na biyar da za su yi da Olympiacos a ƙasar Girka, gola na biyu a ƙungiyar, Andriy Lunin ne zai tsare raga.

Ƙarƙashin sabon kocin Real Madrid, Xabi Alonso, Courtois ne ya kama gola a duka wasanni 17 da suka buga a duka gasanni.

Lunin ɗan asalin Ukraine ne mai shekaru 26, ya taɓa samun damar buga wasanni zamanin tsohon koci Carlo Ancelotti, lokacin da Courtois ya yi jinya mai tsawo.

A yanzu jerin ‘yan wasan Real Madrid da ke jinya sun haɗa da Thibaut Courtois, Dean Huijsen, Antonio Rudiger, David Alaba, Franco Mastantuono, da Eder Militao.

Gasar Zakarun Turai dai fage ne da Madrid ta daɗe tana yin fice. Zuwa yanzu a bana, Real Madrid na da maki 9 daga wasanni 4.