‘Yan bindiga sun sace aƙalla mutum takwas a yankuna uku daban-daban a ƙaramar hukumar Tsanyawa da ke Jihar Kano.
Dan majalisar tarayya mai wakiltar yankin, Injiniya Sani Bala Tsanyawa ya tabbatar wa TRT Afrika da labarin, sai dai ya ce zuwa yanzu ba su kammala tattara alƙaluman yawan mutanen da aka ɗauke ba.
Lamarin ya faru ne da daddare a ranar Litinin, kuma yana zuwa ne a lokacin da ƙasar ke cikin ruɗani na sace mutane a sassa daban-daban na Nijeriya, ciki har da ɗaliban makaranta da masu ibada a cikin coci.
Kafar yada labarai da Daily Trust ta ambato wata majiya a yankin na cewa maharan sun shiga garin ne a ƙafa ɗauke da bindigogi, “sun sace matata da ‘yata mai shekara 17 da matar ƙanina da wasu matan biyu,” in ji shi.
Ya ce sun yi ƙoƙrin dakatar da ‘yan bindigar “amma makaman da muke ɗauke da su ko kusa ba su kai nasu ƙarfi ba tun da su da bindigogi suke zo.”
Ganau din ya ƙara da cewa mazauna yankin sun ankarar da ‘yansanda da sojoji bayan da suka samu raɗe-raɗin cewa ‘yan bindiga suna hanyar garin.
Wani ganau din ya sake gaya wa Daily Trust cewa an kai harin ne ƙauyukan Chibi da Gano da Sarmawa, kuma sun je sauran garuruwan ne a kan babura da yawa.

















