Sojojin Isra'ila sun rusa gidaje da harba makaman atilare a yankuna da ke ƙarƙashin ikonsu a Gaza, suna ƙara saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta.
Shaidu sun faɗa wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa sojojin sun rushe wasu gidaje a unguwar Shujaiya ta birnin Gaza, a arewacin yankin, wanda yake cikin yankin da rundunar ke iko da shi.
A kudu, shaidu sun ce an harba makaman atilare na Isra'ila sassan gabas a Khan Younis waɗanda ba a ƙarƙashin ikon Isra’ila suke ba.
Babu ƙarin bayani kan irin ta’adin da aka yi.
A cewar Hukumar Kariya ta Fararen Hula ta Gaza, an kashe Falasɗinawa biyu kuma wasu da dama sun ji rauni a harin da aka kai wani gida a unguwar Al-Nasr ta birnin Gaza da yammacin Litinin, lokacin da wani bam na Isra'ila ya fashe.
Riyad Mansour, Jakadan Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya, ya shaida wa Kwamitin Tsaro a ranar Litinin cewa tun bayan fara tsagaita wuta a ranar 10 ga Oktoba, sojojin Isra'ila suna kashe yara Falasɗinawa biyu a kowace rana a Gaza, yayin da adadin waɗanda suka jikkata da kuma suka mutu ya kai 1,000, a cewarsa.
A cewar Ma'aikatar Lafiya ta Gaza, aƙalla Falasɗinawa 342 ne aka kashe, kuma kusan 900 sun ji rauni sakamakon hare-haren sojojin Isra'ila, tun lokacin da tsagaita wuta ya fara.
Tun daga Oktoba 2023, sojojin Isra'ila sun kashe kusan mutane 70,000 a Gaza, mafi yawansu mata da yara, kuma sun jikkata fiye da mutane 170,900 a lokacin yakin shekaru biyu na kisan ƙare dangi, wanda ya rusa mafi yawancin yankin.

















