| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
AFCON: Man U za ta rasa Mbeumo, Diallo, da Mazraoui a Disamba da Janairu
Yayin da ya rage wata guda a fara gasar kofin ƙwallon ƙafa na ƙasashen Afirka, AFCON a Morocco, Manchester United ta kwan da shirin rasa 'yan wasa har guda uku a lokacin gasar.
AFCON: Man U za ta rasa Mbeumo, Diallo, da Mazraoui a Disamba da Janairu
Aƙalla 'yan wasa uku ne daga Manchester United za su je gasar AFCON ta 2026
24 Nuwamba 2025

Manchester United ta fara shirye-shiryen maye gurbin ‘yan wasanta uku da za su wakilci ƙasashensu a gasar ƙwallon ƙafa na ƙasashen Afirka, AFCON da za a fara a Morocco.

'Yan wasan guda uku su ne Bryan Mbeumo na Kamaru, da Amad Diallo na Ivory Coast, da kuma Noussair Mazraoui na Morocco.

Za a fara gasar ta AFCON ne daga ranar 21 ga Disamban 2025 zuwa 18 ga Janairun 2026. Kuma tuni tawagogin ƙasashen suka yi wa duka ‘yan wasan kiranye.

Sai dai a halin da ake ciki, kocin Man U na fama da ƙamfar taurarin ‘yan wasan da ke hutun jinya shiga, ciki har da Benjamin Sesko, mai jinyar ciwon gwiwa ta tsawon wata guda.

Akwai ‘yan wasan da a yanzu ba sa samun gurbi a tawagar ta Amorin, kamar Kobbie Mainoo, Joshua Zirkzee, da Manuel Ugarte, waɗanda za su iya cike giɓin da za a samu a Old Trafford.

Sai dai akwai masu sharhin da ke ganin Mainoo da Zirkzee za su iya zaɓar barin ƙungiyar, don neman inda za su samu dama mai ɗorewa ta buga wasanni a-kai-a-kai.

Fatan da Manchester United ke da shi a halin yanzu shi ne, ɗorawa kan nasarorin da take samu, inda ta kwashe wasanni biyar ba a doke ta ba a gasar Firimiya a yanzu.