| hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Burhan ya yi watsi da tayin Amurka na tsagaita a Sudan, ya ce shi ne 'mafi muni a tarihi'
A cikin wani bidiyo da sojoji suka saki a daren Lahadi, Janar Burhan ya ce bai yarda da tayin ba, ya zargi masu shiga tsakani da nuna son kai a ƙoƙarinsu na kawo ƙarshen yaƙin na Sudan.
Burhan ya yi watsi da tayin Amurka na tsagaita a Sudan, ya ce shi ne 'mafi muni a tarihi'
Sudan ta shiga ruɗani a watan Afrilun 2023 lokacin da rikicin ya ɓarke tsakanin sojoji da dakarun ƙungiyar RSF
15 awanni baya

Shugaban Gwamnatin Riƙo na Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya ƙi amincewa da wani tayin tsagaita wuta da masu shiga tsakani ƙarƙashin jagorancin Amurka suka gabatar, yana kiran ta 'mafi muni a tarihi', a yayin da yunƙurin da ake yi na dakatar da mummunan yaƙin da ake yi a ya ƙaru.

A cikin wani bidiyo da sojoji suka sakiea daren Lahadi, Janar Burhan ya ce bai yarda da tayin ba, ya zargi masu shiga tsakani da nuna son kai a ƙoƙarinsu na kawo ƙarshen yaƙin.

Sudan ta shiga ruɗani a watan Afrilun 2023 lokacin da rikicin ya ɓarke tsakanin sojoji da dakarun ƙungiyar RSF a birnin Khartoum da sauran wurare a ƙasar.

Bisa ƙididdigar Majalisar Dinkin Duniya, wannan mummunan yaƙin ya kashe mutane fiye da 40,000, amma ƙungiyoyin agaji suna cewa wannan adadin ya wuce haka. Wannan yaƙin ya haifar da matsalar jinƙai mafi girma a duniya inda yaƙin ya tilasta wa mutum miliyan 14 barin muhallansu.

Hanya mai wahala zuwa zaman lafiya

Ƙasashen huɗu masu shiga tsakani sun kasance suna ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin da dawo da ƙasar a kan hanyar dimokuraɗiyya wadda juyin mulkin soja a shekarar 2021 ya ƙara dagulawa. Ƙasashen sun haɗa da Amurka, Saudiyya, Masar, da Haɗaddiyar Daular Larabawa (UAE).

A wannan watan, Shugaba Donald Trump ya ce yana shirin mayar da hankali wajen taimakawa domin nemo mafita ga yaƙin Sudan bayan Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya Mohammed bin Salman ya roƙe shi ya ɗauki mataki a lokacin ziyararsa a Fadar White House.

Massad Boulos, wani mai ba da shawara a Amurka kan al'amuran Afirka, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP a baya cewa sabon tayin yana kira da a tsagaitawa domin jinƙai na tsawon watanni uku, sai a bi shi da wani tsari na siyasa na watanni tara. RSF ta ce ta amince da tsagaitawar, bayan fushin duniya kan mummunar zaluncin da wasu 'yan ƙungiyar suka aikata a birnin Al Fasher na Darfur.

‘Son kai a shiga tsakani’

Burhan, duk da haka, ya ce tayin ana ɗaukarsa a matsayin mafi muni daga ƙarshe, saboda zai kawar da sojojin ƙasa, ya rushe hukumomin tsaro kuma zai bar dakaru masu riƙe da makamai a wurin da suke — yana nufin RSF.

Idan har shiga tsakanin ya ci gaba ta wannan hanya, za mu ɗauke shi a matsayin shiga tsakani mai nuna son kai, in ji shi.

Ya caccaki mai bayar da shawarar Amurka inda ya zarge shi da ƙoƙarin “tilasta wasu sharuɗɗa a kanmu.” Ya ƙara da cewa: Muna tsoron cewa Massad Boulos zai zama cikas ga zaman lafiya da duka mutanen Sudan suke nema.

A maganganunsa, Burhan ya caccaki UAE. Ya ce tunda a cikin masu shiga tsakani har da ƙasar da ke yankin Gulf, ƙungiyar masu shiga tsakanin “ba za a iya wanke su daga laifi ba musamman bayan duniya ta shiada irin goyon bayan da UAE ta bai wa ‘yan tawaye domin su yaƙi ƙasar Sudan.”

UAE ta musanta cewa tana tallafawa dakarun na RSF.

Burhan ya ƙaryata kuma cewa sojojin suna ƙarƙashin ikon 'yan ta'adda ko cewa sun yi amfani da makaman masu gaba a yaki da RSF — tuhumar da gwamnatin Trump ta yi a watan Mayu.

Burhan ya ce sojojin za su yarda da tsagaitawar wuta ne kawai idan RSF ta janye gaba ɗaya daga yankunan farar-hula don ba da damar 'yan gudun hijira su koma gidajensu, kafin fara tattaunawa don warware rikicin ta hanyar siyasa.

Rumbun Labarai
China ta gargaɗi ‘yan kasarta su kauce wa hadarin zama bayin ma'adinai a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka
Jam’iyyar FPO a Austria ta yi kira da a hana mata yin lullubi
Ghana za ta tura injiniyoyin soji don taimakawa wajen sake gina Jamaica bayan afkuwar guguwa
Mutane 70 sun ɓace bayan jirgin ruwa ɗauke da mutum 120 ya kife a DRC
Wata ƙungiya ta zargi kamfanin Nestle da sayar wa Afirka abincin jarirai mai sikari da yawa
Ranar Makewayi ta Duniya: Kundin tsafta na Afirka don inganta lafiya da mutunci
Sabon Alƙalin Alƙalan Ghana Baffoe-Bonnie ya fara aiki
An raba fiye da mutum 100,000 da gidajensu a Al Fasher na Sudan daga lokacin da RSF ta ƙwace birnin
Kafafen watsa labaran Afirka: Abokan kawo ci gaba da ake mantawa da su
Za a ƙara farashin man fetur a Ghana
Ruftawar mahaƙar ma’adanai ta yi ajalin aƙalla mutum 32 a DRC
An samu rahotanni 32 na yi wa 'yan mata fyade bayan RSF ta ƙwace birnin Al Fasher - Likitoci
Mutum huɗu sun rasu bayan jiragen ruwa biyu na 'yan ci-rani sun kife a gaɓar tekun Libya
DR Congo da M23 sun cim ma yarjejeniyar zaman lafiya 'ta tarihi' a Qatar
AfDB zai ba Nijar CFA biliyan 98.7 domin magance matsalar ruwa ta shekara 70 a Zinder
MDD ta yi gargaɗi kan ƙazancewar yaƙin Sudan, ta yi kira kan barin shigar da kayan agaji
An gabatar da GH¢302bn a matsayin kasafin kuɗin Ghana na 2026 ga majalisar dokokin ƙasar
Sojojin Sudan sun daƙile harin RSF kan filin jirgin sama da dam a arewacin ƙasar
Rubio ya nemi a daina bai wa RSF makamai, ya ɗora wa rundunar laifi kan kashe-kashe a Al Fasher
Dalilin da ya sa TikTok ya goge bidiyoyi miliyan 1.5 da 'yan Uganda suka wallafa