TURKIYYA
2 minti karatu
Babu wani lissafin siyasa ko na tsaro da zai yiwu a duniya ba tare da Turkiyya ba: Erdogan
Yayin da yake magana a “Taron Ƙarni na Turkiyya” a birnin Istanbul, Erdogan ya bayyana irin rawar da Turkiyya ke takawa a duniya inda ya ce ta zama “muryar da ake girmamawa a yankinta da ma duniya baki ɗaya, ƙasar da ke kai wa wasu zaman lafiya.
Babu wani lissafin siyasa ko na tsaro da zai yiwu a duniya ba tare da Turkiyya ba: Erdogan
Erdogan ya ƙara da cewa babban burinsu na dogon lokaci shi ne tabbatar da haɗin kan al'umma da tsaronta / AA
15 awanni baya

Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana cewa babu wani lissafi na siyasa ko na tsaro tun daga Syria zuwa Gaza a Falasdinu, daga yankin Gulf zuwa rikicin Rasha da Ukraine, da za a iya tsarawa ba tare da haɗin gwiwar Turkiyya ba.

Yayi wannan jawabin ne a wurin rufe taron “Taron Ƙarni na Turkiyya” wanda aka gudanar a Cibiyar Taro ta Istanbul a ranar Asabar. Erdogan ya ce Turkiyya ta zama “muryar da ake girmamawa a yankinta da ma duniya baki ɗaya, ƙasa da ke samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.”

Ya jaddada cewa hangen nesa na Ankara ya ta'allaka ne kan tabbatar da makoma inda “ba za a bar kowane ƙarni cikin asara ba, iyaye mata ba za su yi kuka ba, kuma zaman lafiya, tsaro, da wadata za su mamaye dukkan yankinmu.”

Erdogan ya ƙara da cewa babban burinsu na dogon lokaci shi ne tabbatar da haɗin kan al'umma da tsaronta tare da bayar da gudunmawa wajen samar da yankin da ya fi zaman lafiya.

“Tare da haɗin kai, za mu fara gina Turkiyya mara ta'addanci, sannan mu samar da yankin da ba ya fama da ta'addanci a matsayin wani abu mai ɗorewa ga yara ‘yan ƙasa” in ji shi.

Ya kuma sake jaddada cewa ƙasar za ta ci gaba da bin manufofi da suka ta'allaka kan kwanciyar hankali, haɗin kai da zaman lafiya a makwabtanta da ma wajen iyakokinta.