Filin jiragen saman Istanbul ne mafi samun hada-hada a Turai a mako gudan da ya gabata, inda ake da tashi da saukar jirage 1,553, in ji Ministan Sufuri da Zuba Jari na ƙasar Abdulkadir Uraloglu a ranar Juma’a.
Filin jiragen sama na Istanbul ya wuce na Charles de Gaulle da ke Paris, da Frankfurt a Jamus da Heathrow na Landan a tsakanin 23 da 29 ga Yuni.
A jerin sunayen da aka fitar, filin jiragen saman Antalya ne na 10 da yake da tashin jiragen sama 996 a kowace rana.
Uraloglu ya ce rahoton da aka fitar daga Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Jiragen Sama ta Turai da ya kunshi bayanan 23 zuwa 29 ga Yuni, a jimlace Turkiyya ce ƙasa ta shida a jerin ƙasashen Turai a bangaren tashi da saukar jiragen sama, inda take da zirga-zirgar jirage 3,992 a kowace rana, inda ta yi zarra kan ƙasashe irin su Girka, da Netherland, da Poland.
Mahadar yanki da duniya
“A yanzu Turkiyya ba wai ƙasar bi ta cikin ta ba ne kawai a sufurin jiragen sama, ta zama mahaɗar yanki da duniya baki ɗaya.” in ji shi.
Ya bayyana cewa matsakaicin adadin tashi da saukar jiragen sama ya ƙaru da kashi 15 idan aka kwatanta da gabanin annobar Covid-19.
Ya kuma ce Turkiyya na daya daga cikin kasashen da suka koma matakin da suke tun kafin ɓarkewar annobar Korona.
Uraloglu ya kuma bayyana cewa filin jiragen saman Istanbul ne na bakwai a duniya a tsakanin manyan filayen jiragen sama 25, inda take da tashin jiragen sama 773 a tsakanin 23 da 29 ga Yuni.
.png?width=720&format=webp&quality=80)

.png?width=128&format=webp&quality=80)











