Hamshakin attajirin nan na Nijeriya, Jite Odeworitse Tesigimoje, ya janyo ce-ce-ku-ce bayan ya auri matarsa ta 19 a wani biki mai ƙayatarwa.
Attajirin mai shekaru 43 daga jihar Delta mai arzikin man fetur, fitaccen dan kasuwa ne kuma yana yawan kiran a ringa aurar mace fiye da ɗaya. Hotunan bikin aurensa na baya-bayan nan sun yi ta yawo cikin sauri, inda suka haifar da mahawar game da al'adu, da soyayyar zamani.
A wata hira da jaridar The Nation ta Nijeriya, hamshakin mai harkar man fetur ya zayyana falsafarsa, inda ya bayyana zabin aurensa a matsayin sukar ka’idojin ƙasashen yamma kai-tsaye.
Ya ce, “‘Yan mulkin mallaka sun ce mana auren mace ɗaya ne hanya mafi kyau ta rayuwa. Amma kullum suna cikin aikata abin kunya. Me ya sa suke aikata abin da bai dace ba? Me ya sa suka yi mana ƙarya?
Ya ƙara da cewa auren mace fiye da daya ya fi a yaudari mata da yawa a wajen aure.
Attajirin ya ci gaba da bayyana cewa, gidan sa na nuni ne da bambancin ra’ayi da hadin kan Nijeriya, domin ya auri mata daga cikin manyan kabilun kasar da suka hada da Ibo, Yarbawa, Fulani da kuma kabilarsa ta Itsekiri.
'Auren jituwa'
Ko da yake yana son auren mace fiye da ɗaya, Tesigimoje ya yarda cewa ba kowa ne ya cancanci auren mace fiye da ɗaya ba, yana mai cewa yana bukatar “kuɗi mai yawa da kuma hankali.”
Da yake bayyana girman tanadin nasa, hamshakin attajirin ya ce matansa a birnin Lagos na Nijeriya kowacce tana zaune a gida mai ɗaki biyar kuma yana ba su alawus mai tsoka.
Sirrin jituwa, in ji shi, shi ne cikakken adalci. Tesigimoje ya ce, “Da zarar na yi wa mace ɗaya wani abu, dole ne na yi wa sauran ma.”
Mai harkar man ya jaddada cewa wannan daidaiton yana tabbatar da zaman lafiya a gidansa. Ya kuma yi nuni da cewa zai auri mata ta 20.
Duk da cewa auren mace fiye da ɗaya ya zama ruwan dare a Afirka, amma ba kasafai maza suke auren mata da yawa ba kamar yadda Tesigimoje ya yi. Sai dai ba a san adadin ‘ya’yansa ba.
Sai dai masu sharhi da dama sun soki zaɓin nasa, suna masu cewa hakan na ƙara ƙarfafa matsalolin da al’umma ke shiga, abin da kuma zai iya kawo cikas ga bunƙasar tattalin arzikin al'umma.