WASANNI
2 minti karatu
Tawagar Portugal za ta saka jesin karrama tsohon ɗan wasanta bakar fata
Tawagar ƙwallo ta Portugal za ta saka jesi ta musamman don karrama gwarzon ɗan wasanta baƙar fata, Eusébio, wanda ya ci ƙwallaye sama da 700 a rayuwarsa kuma ya ci kyautar Ballon d'Or a 1965.
Tawagar Portugal za ta saka jesin karrama tsohon ɗan wasanta bakar fata
Za a buga samfurin jesin kwafi 1,965 kacal, mai ɗauke da lamba 13, wato lambar jesin Eusébio. Hoto: Getty
4 Nuwamba 2025

Ba a fiya samun ‘yan wasan ƙwallo da suka kai matsayin a ce an yi jesi ta musamman don karrama su ba. Amma hakan ne zai faru a tawagar Portugal, wadda za ta karrama tsohon ɗan wasanta, marigayi Eusébio, wanda ya mutu a 2014.

Eusébio ɗan wasan tsakiya da "Pantera Negra", wato Baƙar Damisa ya kasance tauraro kuma ja-gaban tawagar ƙasar Portugal a shekarun 1960 zuwa farkon 1970, wanda kuma ya rasu a 2014.

Ɗan wasan ya jagoranci ƙungiyarsa ta Benfica wajen lashe kofuna a gasar ƙasar sau 11, da tarin kofuna a cikin gida, da kuma Kofin Turai a 1961-62.

Eusébio ya yi suna wajen salon wasansa da kuzarinsa da hazaƙa, inda ya zamo cikin jerin waɗanda suka fi zura ƙwallaye a duniya, da ƙwallaye sama da 700 a rayuwarsa.

Ya ciyo wa Portugal ƙwallaye 41 a wasanni 64, inda ya kafa tarihin da ba a zarta shi ba sai lokacin ɗan wasa Pauleta, sannan daga baya Cristiano Ronaldo ya kafa nasa.

Lokacin da Ronaldo ya ci ƙwallonsa ta 400 kwanaki uku bayarn mutuwar Eusébio ranar 5, ga Janairun 2014, ya ce, “Na sadaukar da ƙwallayen nan ga Eusebio. Na kasance makusancinsa sosai kuma ya taimake ni matuƙa.

Shekaru 60 da cin Ballon d'Or

Domin tunawa da shekaru 60 byana da Eusébio ya zama ɗan wasan Portugal na farko da ya ci kyautar gwarzon ƙwallon ƙafar duniya Ballon d'Or a1965, kamfanin kayayyakin wasanni na Puma ya tsara kayan wasa na musamman waɗanda tawagar ƙasar Portugal za ta saka.

Shirin ya samu amincewar iyalai da dangin Eusébio, inda matar marigayin, Flora Bruheim, ta ce ta ji “matuƙar daɗi" da karramawar.

Jesin da za su saka baƙa ce wuluk da ɗan zirin launin zinare, don tunawa da ɗan wasan da kuma ake masa laƙabi da "O Rei", wato “Sarki”, irin laƙabin da ake wa shahararren ɗan wasan Brazil Pelé.

Za a buga samfurin jesin kwafi 1,965 kacal, mai ɗauke da lamba 13, wato lambar jesin Eusébio.

Sai a ranar 16 ga Nuwamba ne tawagar ta Portugal za ta saka jesin a birnin Porto, inda za su yi wasa da Armenia na neman cancantar buga gasar Kofin Duniya.