GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Trump ya ce “nan ba da jimawa ba” za a samar da dakarun tsaro na ƙasa da ƙasa a Gaza
"Gaza na tafi yadda ya kamata," a cewar Shugaban Amurka a wani taro na fadar White House da shugabannin tsakiyar Asiya ranar Alhamis.
Trump ya ce “nan ba da jimawa ba” za a samar da dakarun tsaro na ƙasa da ƙasa a Gaza
Trump ya nuna cewa runduna ta zaman lafiya ta ƙasa da ƙasa za ta iya isa Gaza “nan ba da jimawa ba”.
8 awanni baya

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana sa rai dakarun tsaro na ƙasa da ƙasa da Amurka ke haɗawa za su kasance a Gaza "nan ba da jimawa ba," bayan shekara biyu na yaƙin isra’ila a Zirin da aka yi wa ƙwanya.

"Zai kasance nan ba da jimawa ba. Kuma Gaza na tafiya yadda ya kamata," kamar yadda Trump ya bayyana a wani zaman fadar White House da wasu shugabannin tsakiyar Asiya da yammacin ranar Alhamis, inda yake magana kan rundunar tsaro na bayan yaƙi da ake sa ran ƙaddamarwa a Gaza. 

Amurka ta gabatar da wani daftarin ƙudirin Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ga ƙasashe abokan hulɗa domin ƙarfafa shirin zaman lafiyar Trump a Gaza mai batutuwa 20 ciki har da ba da izini ga rundunar tsaro ta ƙasa da ƙasa, kamar yadda ofishin jakadancin Washington ya bayyana ranar Laraba.

Jakadan Amurka Mike Waltz ya gabatar da daftarin ga mambobi goma da aka zaɓa daga kwamitin tsaro da sauran ƙasashe masu ƙarfi a yankin — Turkiyya da Masar da  Qatar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da kuma Saudiyya — kamar yadda wani mai magana da yawun Amurka ya faɗa ranar Laraba.

Ba a tsayar da ranar kaɗa ƙuri’a kan daftarin ba.

“Samar da sakamako”

Sanarwar ta Amurka ta ce ƙudurin "ya bai wa dakarun tsaro na ƙasa da ƙasa izinin”,  da aka bayyana a cikin tsarin na zaman lafiya. 

Majiyoyin diflomasiyya sun ce wasu ƙasashe sun nuna son ba da gudunmawa wajen ba da dakarun na ƙasa da ƙasa (ISF)  amma suna son sa hannun kwamitin tsaro na MDD kafin su tura dakaru Falasɗinu.

"A ƙarƙashin shugabancin jarumtaka na Shugaba Trump, Amurka za ta sake samar da samakamo a MDD — ba maganganu mara kyawu ba," in ji mai magana da yawun Amurka.

Kafa dakarun tsaro na ƙasa da ƙasa wani muhimmin ɓangare ne na yarjejeniyar tsagaita wuta ta ranar 10 ga watan Oktoba tsakanin Isra’ila da ƙungiyar gwagwarmaya ta Hamas.

A ƙarƙashin yarjejeniyar, dakarun da za a samar daga ƙasashen Larabawa da Musulmai za a tura su Gaza ne domin tabbatar da tsaro yayin da sojojin Isra’ila suka janye.

Yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan Gaza, dakarun Isra’’ila sun kashe wani yaro Bafalasɗine mai shekara 15 a wani kutsen soji a garin Al-Yamun, yamma da Jenin, a yankin Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye, da safiyar ranar Alhamis, in ji kamfanin dillancin labaran WAFA.