Da yake jawabi a gaban Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya karo n 80, Shugaba Erdogan ya yi abin da ya wuce batun sukar yakin Isra’ila a Gaza; ya kalubalanci MDD kanta, ya zargi tsarin duniya da hadin baki, tare da bayyana Turkiyya a matsayin mai kokarin gyara tsarin da ya lalace.
Jawabin nasa ya wuce yin Allah wadai da kisan kare dangi a Gaza; wani yunkuri ne na sake fasalin rawar da Turkiyya ta taka a matsayin mai nuna yadda ya kamata a yi da karfi a yankin a daidai lokacin da duniya ke fama da rauni.
Yayin da Gaza ta mamaye kalaman nasa, Erdogan ya yi amfani da zauren majalisar wajen sanya rikicin cikin wani hoto mai girma.
Ya tabo Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya don nuna gazawar Majalisar wajen tabbatar da manufar samar da zaman lafiya da tsaro, ya gode wa kasashen da suka amince da Falasdinu, ya kuma bukaci sauran su yi koyi da hakan.
Ta hanyar yin haka, ya bayyana karara cewa shawarar da Turkiyya ke bayarwa na samar da kasashe biyu ba abu ne na je ka na yi ka ba, hakan ginshiki ne na manufofinta a kasashen ketare, mai kalubalantar abin da Ankara ke gani a matsayin gaza sauke nauyin da Majalisar Dinkin Duniya ta dauka.
Erdogan ya dan yi shiru don bayyana alhininsa na rashin halartar shugaban hukumar Falasdinu Mahmoud Abbas zuwa taron na MDD saboda kin amincewar da Amurka ta yi na ba shi visa tare da jami'an Falasdinawa kusan 80.
Kawo batun Abbas ya bayyana yadda Turkiyya ke goyon bayan samar da kasashe biyu da kuma yadda Ankara ke ba da taimako wajen samar da yanayin da za a cim-ma a zance da kuma a aikace.
Daga nan, Erdogan ya juya ga ayyukan barna da Isra'ila ke yi, yana mai cewa hare-haren ba wai ga farar hula kawai suka tsaya ba, suna kai wa dukkan rayuwar falasdinawa baki daya; dabbobi, gonaki,tsaffin itatuwan zaitun, da hanoyin samar da ruwa.
Ta hanyar jaddada waɗannan cikakkun bayanai, ya nemi ya nuna wa duniya cewa abin da ake kai wa hari ba kawai mutane ba ne, dukkan rayuwar ce baki daya.
Ya kuma jaddada yadda kisan kiyashin da ake yi a Gaza ke kara zurfafa, inda ya bayyana cewa ana ci gaba da yin kisan kiyashi duk da taron Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana.
"A cikin watanni 23 da suka gabata, an kashe yaro guda a kowace sa'a a Gaza," in ji shi, kafin ya nuna wa wakilai hotunan yaran Falasdinawa da ke fama da yunwa.
Wadannan hotuna sun bayyana gaskiyar yadda Isra'ila ta yi watsi da mafi yawan bukatun bil'adama da na rayuwa a kokarinta na hana aiwatar da manufofin sasanta kasashen biyu.
"Babu yaki a Gaza, ba za a iya magana game da kasancewar bangarori biyu ba. A gefe guda, akwai sojoji na yau da kullun da mafi yawan makamai na zamani, sannan a daya bangaren kuma, akwai fararen hula marasa laifi.
“Wannan ba yaki ne da ta'addanci ba, siyasa ce ta raba mutane da matsugunansu, gudun hijira, kisan kiyashi, da kisan gilla, ta yin amfani da abin da ya faru a ranar 7 ga Oktoba a matsayin hujja," in ji Erdogan.
Kalaman nasa ƙalubale ne kai tsaye ga ƙoƙarin da Isra'ila ke yi na lulluɓe mamayar da take yi da kuma mamaye ta a ƙarƙashin tutar manufofin tsaro.
Da yake ci gaba da tabo wannan batu, shugaban na Turkiyya ya bayyana irin ayyukan da Isra'ila ke yi a Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye, inda Hamas ba ta da iko, don nuna hujjojin da Isra'ila ta kirkira na cewa matakan sojan da take dauka na yaki da ta'addanci ne.
Wani abin lura a cikin jawabin na shugaba Erdogan shi ne furucinsa na cewa ayyukan Isra'ila suna lalata nasarorin da dukkan bil'adama suka samu. "Wadanda suka yi shiru suna da hannu cikin wannan ta'asa," in ji shi.
Illar ta fito fili: Gaza ba wai rayuwar Falasdinawa ba ce kawai amma game da mutuncin bil'adama kansa, kuma amincin Majalisar Dinkin Duniya ya dogara ne akan ko za ta dauki mataki.
Shugaban na Turkiyya ya jaddada cewa, za a iya kiyaye wannan mutunci ta hanyar hadin gwiwa da daukar matakan dakile ayyukan kisan kiyashi da ake yi.
Ya kuma yi gargadi da kakkausar murya cewa Isra'ila barazana ce ga zaman lafiya a yankin, yana mai bayyana cewa ba za a iya barin wannan "hali na hauka" ya ci gaba ba.
Daga Gaza zuwa yankin
Erdogan ya kuma fadada bayanan zuwa wajen Gaza, inda ya bayyana yakin Isra'ila a matsayin wata babbar ajandar fadada da mamaya a yankin.
Tabbas, shekaru biyu da suka gabata, a wurin taron Majalisar Dinkin Duniya irin wannan, Firaminista Benjamin Netanyahu ya gabatar da taswirorin da ke nuna mamaye Yammacin Kogin Jordan da Gaza a matsayin wani ɓangare na Isra’ila, abin da mutane da yawa suka gani a lokacin yana haɓaka ra’ayin samar da “Babbar Kasar Isra’ila.”
Yanzu, shugaban kasar Turkiyya ya lissafa hare-haren da Isra'ila ke kai wa Syria, Lebanon, Yemen, Iran, Qatar, yana mai gargadin cewa hargitsin Gaza lamari ne da ya shafi yankin baki daya.
A taron Falasdinu da aka gudanar a gefen babban taron Majalisar Dinkin Duniya, Erdogan ya kara da cewa: Gwamnatin Netanyahu da ke mulkin al'ummar da ake son kawar da su ta hanyar kisan kiyashi, tana aiwatar da kisan kiyashi ga makwabtanta na dubban shekaru, wadanda suke da kasa, ruwa, iska, da teku tare da su.
Daga cikin wadannan kalamai an samu wata gaba ta tarihi: "Mun kuma zauna a wannan kasa tsawon dubban shekaru.
Mun yi tarayya da da iyaka ta kasa, ruwa, teku, da iska. Amma wannan rabon dole ne ya kasance na gaskiya, daidaito, da kuma adalci, ba wai kawai mayar da hankali ga bangare ɗaya ba."
Ta hanyar ambaton "dubban shekaru," Erdogan ba wai kawai ya ki amincewa da burin Netanyahu na "Ƙasar Alkawari", "Babbar Kasar Isra'ila", amma yana gargadin cewa wata rana kisan kiyashi a Gaza na iya isa ga iyakokin kasashe makwabta.
Jawabin na Erdogan mai karfi na Majalisar Dinkin Duniya ya sake mayar da Turkiyya a matsayin mai kare adalcin kasa da kasa, mai kare ikon yankin, da kuma salon tsarin Majalisar Dinkin Duniya wanda sau da yawa ya gaza aiki da ka’idojinsa.
Ko mutum ya yarda da tsarinsa ko a'a, jawabin yana nuna aniyar Ankara na da'awar babbar rawar da za ta taka wajen tsara labarun dabi'un kirki da dabarun bayar da labaran Gabas ta Tsakiya. A wajen Erdogan, Gaza ita ce zakaran gwajin dafi, amma abin ya yi nisa.