| hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
'Musulmai ne Boko Haram ta fara yi wa ɓarna': AU ta yi watsi da Trump kan kisan kiyashi a Nijeriya
A farkon wannan watan Trump ya umarci Ma'aikatar Yaƙi ta Amurka ta soma shirye-shiryen yiwuwar kai hari Nijeriya bayan da ya yi zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a ƙasar.
'Musulmai ne Boko Haram ta fara yi wa ɓarna': AU ta yi watsi da Trump kan kisan kiyashi a Nijeriya
Shugaban hukumar ƙungiyar tarayyar Afirka Mahmoud Ali Youssouf yayin da yake jawabi a Villa Doria a birnin Rome ranar 20 ga watan Yunin shekarar 2025
6 awanni baya

Shugaban Ƙungiyar Haɗin kan Afirka (AU) ya yi watsi da iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Nijeriya, yana mai cewa zargin ba gaskiya ba ne.

Da yake jawabi ga manema labarai a Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin New York ranar Laraba, Mahmoud Ali Youssouf ya ce hasali ma "Musulmai ne na farko da mayaƙan Boko Haram suka kai wa hare-hare ba Kiristoci ba", yana mai jaddada cewa ba a yi wa Kiristoci kisan kiyashi a ƙasar da ta fi yawan mutane a Afirka..

"Abin da yake faruwa a arewacin Nijeriya ba shi da wata alaƙa da irin zaluncin da muke gani a Sudan ko kuma a wasu sassan Gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo," kamar yadda Ali Youssouf ya bayyana, yana mai ishara ga Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.

"Ya kama mutum ya yi tunani kafin ya yi irin wannan maganar," in ji shi. "Waɗanda harin Boko Haram ya fara yi wa ɓarna Musulmai ne, ba Kiristoci ba."

Ƙungiyar Boko Haram ta ‘yan bindiga masu tsattsauran ra’ayi ta kwashe fiye da shekara 15 tana aikata ta’addanci a arewa maso gabashin Nijeriya, inda ta kashe dubban mutane.

Masu AlakaTRT Afrika - Trump ya umarci Ma'aikatar Yaƙi ta Amurka ta soma shirin yiwuwar kai hari Nijeriya

Masana kan ‘yancin ɗan’adam sun ce yawancin waɗanda hare-haren Boko Haram suka shafa Musulmai ne.

A farkon wannan watan Shugaban Amurka Donald Trump ranar Asabar ya umarci Ma'aikatar Yaƙi ta ƙasar ta soma shirye-shiryen yiwuwar kai hari Nijeriya bayan da ya yi zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a ƙasar.

Trump ya bayar da umarnin ne a saƙon da ya wallafa a shafinsa na Truth Social kwana guda bayan ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 a Nijeriya ba tare da ya bayyana takamaimai inda ya samu waɗannan alƙaluma ba.

“Muddin gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da dukkan tallafin da take bai wa Nijeriya nan-take, kuma mai yiwuwa za ta shiga wannan ƙasƙantacciyar ƙasar, cike da ƙarfin gwiwa domin kawar da 'yan ta'adda masu kaifin kishin Musulinci waɗanda ke yin wannan ta’asa,” in ji Trump.

Ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya ta ce ƙasar za ta ci gaba da yaƙarmasu tsattsaurar ra’ayi kuma tana fatan cewa Washington za ta ci gaba da kasancewa abokiyar tarayyarta ƙut da ƙut.

Kazalila ta ce za "ta ci gaba da kare dukkan ‘yan ƙasa, ba tare da la’akari da ƙabila ko aƙida ko kuma addini ba".

Nijeriya, wadda ke da fiye da ƙabilu 200 da suke gudanar da addinai na Kiristanci da Mulunci da ma addinan gargajiya tana da tarihi mai tsawo na zaman lafiya tare.

Amma ta sha fuskantar tashe-tashen hankula na ƙabilanci da addini.

 

Rumbun Labarai
Jiragen yaƙin Nijeriya sun kashe ‘yan ta’addan ISWAP da ɓarayin daji a Borno da wasu jihohin Arewa
Babu abin da za mu rasa idan Nijeriya ta daina hulɗa da Amurka – Sheikh Gumi
Damuwa kan kutsawar 'yan bindiga Jihar Kano
Rundunar sojin Nijeriya ta ce ta kuɓutar da mutum 86 da Boko Haram ta yi garkuwa da su
INEC ta ayyana Charles Soludo na APGA a matsayin wanda ya lashe zaɓen Gwamnan Anambra
Gwamnatin Nijeriya ta amince a ci bashin dala 396 domin inganta kiwon lafiya da ayyukan jinƙai
An gabatar da kudiri a Majalisar Dokokin Amurka don saka wa Ƙungiyoyin Miyetti Allah takunkumi
‘Kisan kiyashi ga Kiristoci: Me ya sa kurarin Trump a Nijeriya yake kan kuskure da rashin dacewa?
Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince a ɗaure malaman makaranta shekara 14 kan cin zarafin ɗalibai
An kashe 'yan ta'adda fiye da 592 a Borno tun daga Maris din 2025 - Ministan Yada Labaran Nijeriya
ECOWAS ta yi tir da ikirarin ‘ƙarya mai hatsari’ na Amurka cewa Nijeriya ta bari ana kashe Kiristoci
Hukumar DSS a Nijeriya ta kori ma'aikatanta fiye da 100
Amurka na da ajanda a Nijeriya tana fakewa da kisan Kiristoci - Sheik Bala Lau
China na adawa da Trump kan amfani da 'addini da ‘yancin ɗan'adam' domin tsoma baki a Nijeriya
Naira da hannayen-jari Nijeriya sun faɗi sakamakon barazanar da Trump ya yi ta kai hari ƙasar
Jami'an tsaron Nijeriya sun hallaka 'yan bindiga 19 a Jihar Kano
Yadda barazanar da Trump ya yi kan aika sojoji Nijeriya ta tayar da ƙura
Dakarun Nijeriya sun kuɓutar da mutanen da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su Jihar Kogi
Ya kamata Amurka ta taimaka wa Nijeriya da makamai maimakon barazana —Kwankwaso
Muna shirin ɗaukar mataki kan Nijeriya - Sakataren Ma’aikatar Yaƙi na Amurka