Saɓanin da ya kunno kai tsakanin Majalisar Dattijan Nijeriya da Shugaba Tinubu kan janye 'yansanda
NIJERIYA
3 minti karatu
Saɓanin da ya kunno kai tsakanin Majalisar Dattijan Nijeriya da Shugaba Tinubu kan janye 'yansandaSanatocin sun bayyana damuwa kan cewa yayin da aka janye musu ‘yansandan da ke kare su, wasu manyan mutane har yanzu suna samun wannan kariyar da ‘yansanda ke bayarwa.
Rais wa Nigeria Bola Tinubu ametangaza hali ya dharura kufuatia utekaji nyara wa watu wengi. / / Reuters
kwana ɗaya baya

An samu saɓani tsakanin Shugaba Tinubu da ‘yan majalisar dattijai game da batun janye ‘yansanda da ke ba da kariya ga manyan mutane.

A ranar Laraba ne Majalisar Dattijan Nijeriya ta nuna damuwa game da abin da wasu sanatoci suka bayyana a matsayin zaɓe wajen aiwatar da umarnin Shugaba Tinubu na janye ‘yansanda daga aikin bai wa manyan mutane kariya domin taimakawa wajen daƙile matsalar rashin tsaron da ƙasar ke fama da ita.

Sanatocin sun bayyana damuwa kan cewa yayin da aka janye musu ‘yansandan da ke kare su, wasu manyan mutane har yanzu suna samun wannan kariyar da ‘yansanda ke bayarwa.

Ƙorafinsu na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ke jaddada neman cikakkiyar biyayya ga umarnin da ya bayar na farko na janye dukkan ’yansanda daga kula da manyan mutane a faɗin ƙasar.

Shugaban ya kuma umarci Ministan Tsaron Cikin Gida da Sufeto Janar na ‘yansanda da rundunar tsaron al’umma ta NSCDC da su tabbatar da cewa an maye gurbin jami’an ‘yansanda da ke aiki na musamman saboda ka da a ƙyale mutane ba tare da kariya ba.

‘Yanmajalisar wadanda suka yi fushi kan rashin aiwatar da umarnin janye ‘yansandan gabaɗaya duk da cewa Sufeto Janar na ‘yansandan Nijeriya, Kayode Egbetokun ya sha alwashin kama duk wani jami’in ‘yansandan da ya keta wannan umarnin, sun yi kira da a tabbatar da cewa an janye wa kowa ‘yansanda domin tabbatar da adalci da daidaito.

Yayin da sanatocin ke ƙorafi cewa wasu ‘ya’yan masu riƙe da muƙaman siyasa har yanzu suna da dogarai ‘yansanda da kariyar tsaro, sun nemi su ma a cire su daga cikin waɗanda umarnin zai shafa domin ka da wata matsala ta faru da su.

Ƙorafin ya fito daga ƙudirin da Sanata Abdul Ningi mai wakiltar jihar Bauchi ta tsakiya ya gabatar a zauren majalisar.

Sanata Ningi ya sanar da majalisar cewa dogari ɗansanda ɗaya tilo da yake da shi an janye shi a ranar Laraba da safe yayin da wasu manyan mutane a ƙasar suke ci gaba da cin moriyar wannan alfarmar ta amfani da ‘yansanda a matsayin dogarai.

Ningi ya ce shi ya ga tawagogin ministoci da ‘ya’yan masu riƙe da muƙaman siyasa da ‘yan kasuwa ‘yan China da mawaƙa suna yawo da dogarai ‘yansanda.

Duk da cewa Sanata Ningin ya ce shi zai iya kare kansa, amma ya kamata a janye wa kowa ta yadda wannan tsarin zai zama mai adalci.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattajai, Sanata Barau Jibrin wanda ya jagoranci zaman ya ce shugabannin majalisar sun tattauna a kan lamarin a ranar Talata kuma suna ƙoƙarin gamsar da Fadar Shugaban Ƙasa ta ware sanatoci daga cikin waɗanda umarnin janye ‘yansanda zai yi aiki a kansu.

Ya ce suna da ƙwarin gwiwar cewa Shugaba Tinubu zai saurare su kuma in Allah Ya yarda zai mayar musu da ‘yansandansu.

Sai dai kuma Shugaba Tinubu ya ba da umarnin cikakkiyar biyayya ga umarnin da ya bayar daga farko na janye dukkan ‘yansanda daga manyan mutane a faɗin ƙasar.

Tinubu, wanda ya ba umarnin a kalamansa kafin a fara taron majalisar zartarwa a Abuja, ya ce yayin da ƙasar ke fuskantar garkuwa da mutane da ta’addanci ya kamata ta yi amfani da dukkan dakarunta domin kare ‘yan Nijeriya.

A yanzu dai ‘yan Nijeriya za su sa ido inda za su so ganin yadda lamarin tsaron ƙasar zai gyaru ta wannan matakin da shugaban ƙasar ke son ɗauka.