Shugaban Kasar Kamaru Paul Biya, shugaban da ya fi kowane dadewa a kan mulki a duniya, wanda ya hau shugabanci fiye da shakaru 40 da suka gabata, ya sake karbar rantsuwar sabon wa’adin mulki na takwas.
Wa'adi bakwai a jere. Shekaru arba'in yana mulki. Kuma bai gama ba tukuna. Paul Biya, shugaban Kamaru da ya fi kowane shugaba dadewa a kan mulki, ya fara sabon wa'adi, wanda zai iya ci gaba da rike shi har zuwa lokacin da ya cika shekaru 99.
Yana da shekaru 92, Biya shi ne shugaban da ya fi tsufa a duniya, kuma shugabanni kaɗan ne kawai suka yi irin daɗewarsa a mulki. To, ta yaya ya yi hakan?
''Yana da wayo sosai, musamman idan ana maganar siyasa. Ya san yadda ake tafiyar da lamarin,'' in ji Dr. Therence Atabong Njuafac, wata mai sharhi kan siyasa a Kamaru, yayin tattaunawa da TRT Afrika.
Dabaru ne da ya dinga amfani da su fiye da shekaru 40. A shekarar 1982, Biya ɗan siyasa ne da ba a san shi sosai ba lokacin da shugaban Kamaru na farko Ahmadou Ahidjo ya yi murabus ba zato ba tsammani.
Biya ya shiga harkokin mulki inda har zuwa yau ya ki sauka. Ya tsallake yunƙurin juyin mulki da dama, ya fi abokan hamayya iya makirci, kuma ya dakatar da yunkurin 'yan-aware a yankunan arewa maso yamma da kudu maso yammacin Kamaru.
Mamaye harkokin mulki
"Komai irin kukanku, a koyaushe yana da mafita ga matsalarku," in ji Njuafac.
A cewar Ahmadou Shehou Orges, dabarun Paul Biya masu ƙarfi su ne sanya manyan cibiyoyin gwamnati a ƙarƙashin kulawarsa tare da abokan aikinsa.
"Mamaye harkokin mulki ne abin da ya yi don ci gaba da mulki. Mafi mahimmancin sassa a ƙasar suna ƙarƙashin Biya. Majalisar Tsarin Mulki ma na ƙarƙashinsa," Shehou Orges ya shaida wa TRT Afrika.
Kuma lokacin da wani sauyi a kundin tsarin mulki a 2008 ya soke kayyade wa'adin mulki, hakan ya tabbatar da aniyarsa. Biya zai iya mulki har abada.
"Don haka babu iyaka. Babu iyakance wa'adi ga shugaban ƙasa, 'yan majalisa, ko jami'ai. Za su iya ci gaba da mulki, za su iya mulki yadda suke so... har abada," in ji Shehou Orges.
Yayin da Biya ya fara wa'adinsa na 8, babban ɗan takarar adawa Issa Tchiroma Bakary da magoya bayansa suna ci gaba da ƙalubalantar nasarar shugaban a zaɓen 12 ga Oktoba.
‘Yan adawa da aka raunata
Sau da yawa ana kwatanta mulkin Biya da wasan dara da ake yi sannu a hankali, cikin dabaru da haƙuri. Magoya bayansa sun ce ya sanya Kamaru zama cikin kwanciyar hankali a yankin da ke cikin rikici.
Amma masu suka na cewa "kwanciyar hankali" da kasar ke da shi ya samu ne saboda tsarin dimokuradiyya. Sau da yawa ana toshe muryoyin 'yan adawa ko kuma a raunana su.
‘"Tsarin samar da jam’iyyu da yawa dabara ce ta rarraba kawunan ‘yan adawa. Wannan ita ce ɗaya daga cikin hanyoyin da ake bi don tabbatar da Biya ya ci gaba da mulki," in ji Njuafac.
An haife shi a shekarar 1933. Iyayensa ‘yan mishan ne da suka rayu a kudancin Kamaru, Biya ya taɓa yin burin zama babban malamin coci. Amma kuma, ya yi karatun shari'a da siyasa a Paris kuma ya sami karfin gwiwar yin mulki.
Yanzu, yayin da yake fara wani sabon wa'adi, dukkan idanu suna kan Kamaru da kuma mutumin da ya mallaki fagen siyasar kasar fiye da shekaru 40.
A shugabancin da ya fi dadewa a duniya, kowane mataki yana da muhimmanci.



















