WASANNI
3 minti karatu
‘Yan Nijeriya uku za su taka leda a Gasar Zakarun Turai ranar Laraba
Ɗaya daga cikin ‘yan Nijeriyar da za su fafata shi ne Victor Osimhen wanda ke buga wasan gaba Galatasary na ƙasar Turkiyya.
‘Yan Nijeriya uku za su taka leda a Gasar Zakarun Turai ranar Laraba
Osimhen ne ya zura wa Galatasaray ƙwallo a ragar Liverpool a nasarar da ƙungiyar ta Turkiyya ta yi a kan Zakarun Gasar Firimiya / Reuters
6 awanni baya

A ci gaba da wasannin Zakarun Turai ‘yan wasan Nijeriya uku suna cikin waɗanda za su fafata a ranar Laraba da yamma.

Ɗaya daga cikin ‘yan Nijeriyar da za su fafata shi ne Victor Osimhen wanda ke buga wasan gaba Galatasary na ƙasar Turkiyya.

Osimhen a Turkiyya

Osimhen zai yi burin ci gaba da zurawa ƙwallaye a raga kamar yadda ya yi a wasan Nijeriya da Jamhuriyar Benin da yammacin ranar Laraba lokacin da Galatasayar za ta karɓi baƙuncin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta FK Bodø/Glimt daga ƙasar Noway.

Osimhen wanda ya shi ya ci ƙwallo ɗaya tilo da Galatasay ta zura a ragar Liverpool a karawar da ƙungiyar ta Turkiyya ta samu nasarar a kan zakarun Gasar Firimiyar Ingila, zai so ya ci gaba da taimaka wa ƙungiyar tasa samun irin wannan nasarar.

Ademola a Italiya

Kazalika shi ma ɗan wasan gaban Nijeriya, Ademola Lookman zai kasance cikin ‘yan wasan da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Atalanta za ta dogara da su a fafatawar da za ta yi da yammacin Laraba da ƙungiyar ƙwallon ƙafarsa ta Atalanta ta Italiya za ta karɓi baƙuncin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Slavia Praha ta ƙasar Check.

Gwarzon ɗan wasan Afirka mai ci, Ademola Lookman, zai kasance cikin wasan da za su taka leda ranar Laraba a filin wasa na Geiss da ke Italiya da yammacin ranar Laraba.  

Duk da cewa Atalanta ta fara Gasar Zakarun Turai ta kakar bana ne da ƙafar hagu inda PSG ta lallasa ta da ci 4 da nema, ta samu ta yi nasara kan ƙungiyar Club Brugge da 2-1.

Ademola Lookman zai so ya gamsar da masoaya ƙwallo cewa ba banza ya zama gwarzon ɗan wasan Afirka a shekarar da ta gabata ba.

Raphael Onyedika a Jamus

Shi kuma dan wasan tsakiyar Nijeriya, Raphael Onyedika, da ke taka leda a ƙungiyar Club Brugge zai nuna bajintarsa ne a Jamus inda ƙungiyarsa za ta je ta kara da ƙungiyar Bayern Munich a filin wasa na Allianz Arena.

Bayern Munich ta yi nasara a wasanninsu biyu na farko sun yi nasara kan ƙungiyoyin Chelsea da Pafos, yayin da Club Brugge ta lallasa Monaco da ci 4-1 a wasanta na farko kafin ta sha kaye a hannun Atalanta.

Onyedika ya kasance ɗaya daga cikin mahimman ‘yan wasan Club Brugge a wannan kakar, inda ya buga wasannin tara cikin dukkan gasa wa ƙungiyar.

Ya zura ƙwallo a raga a nasarar 4-1 da ƙungiyar ta yi kan Monaco, kuma zai yi fatan ƙara yawan ƙwallayensa a kan ƙungiyar Bayern Munich watta take cin ƙwallaye.