AFIRKA
2 minti karatu
Amurka ta buƙaci a tattauna domin kawo ƙarshen yaƙin Sudan, ba amfani da ƙarfin soja ba
“Babu wata mafita da za a samu ta hanyar amfani da soji, sannan tallafin soji daga waje zai ƙara tsawaita rikicin ne kawai,” in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka a yayin da take Allah wadai da munanan laifukan da RSF ta aikata a Al Fasher.
Amurka ta buƙaci a tattauna domin kawo ƙarshen yaƙin Sudan, ba amfani da ƙarfin soja ba
Over 62,000 people were displaced after RSF seizes control of Al Fasher in Sudan’s North Darfur. / AA / AP
21 awanni baya

Amurka ta yi Allah wadai da munanan laifukan da dakarun sa kai na Rapid Support Forces (RSF) suka aikata a Al Fasher, Arewacin Darfur, tana kuma kira ga dukkan bangarorin Sudan su “bi hanyar tattaunawa don kawo karshen wahalhalun da mutanen Sudan ke fuskanta.”

“Amurka ta yi Allah wadai da rahotannin munanan laifukan da aka ce dakarun RSF sun aikata a El Fasher, Arewacin Darfur,” in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka a wani rubutu da ta wallafa a X ranar Asabar.

Ta kara da cewa Washington tana “matukar damuwa” game da tsaron fararen-hula da suka makale a cikin birnin da kuma waɗanda ke tserewa zuwa yankunan makwabta yayin da rikici ke kara kamari.

“Dole RSF ta daina ɗaukar fansa da tashin hankali na kabilanci; ba za a sake maimaita mummunan abin da ya faru a El Geneina ba,” in ji sanarwar.

“Babu wata mafita da za a samu ta hanyar amfani da soji, sannan tallafin soji daga waje zai ƙara tsawaita rikicin ne kawai,” kamar yadda ta kara da cewa.

Dubban mutane sun mutu

Tun daga watan Afrilun 2023, dakarun RSF suka fara yaki da sojojin gwamnati, kuma a ranar Lahadi suka kwace Al Fasher, suka kori sojojin daga sansaninsu na karshe a Darfur bayan watanni 18 na kunci da hare-haren bama-bamai.

Tun bayan ƙwace birnin, an samu rahotannin kashe ɗumbin mutane, cin zarafin mata, hare-hare kan ma'aikatan agaji, fashi da garkuwa, yayin da hanyoyin sadarwa kusan suka katse baki ɗaya.

Rikicin ya kashe kimanin mutane 20,000 kuma ya raba sama da miliyan 15 da muhallansu, bisa ga rahotannin Majalisar Dinkin Duniya da na cikin gida.

Da safiyar Asabar, kungiyar likitoci ta Doctors Without Borders (MSF) ta nuna damuwa kan rayukan dubban fararen hula da suka makale a cikin Al Fasher bayan dakarun RSF sun karbe ikon birnin.

MSF ta ce tawagoginta a Tawila sun shirya don kula da yawan mutanen da suka rasa matsugunansu da kuma wadanda suka jikkata bayan birnin ya fada hannun RSF.