Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya fara hutun shekara-shekara ranar Alhamis 4 ga watan Satumba na wannan shekarar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Nijeriya, Bayo Onanuga, ya wallafa a shafinsa na X, ta ce shugaban zai shafe kwanakin aiki goma yana hutun na shekara-shekara.
“Shugaba Tinubu zai yi hutun ne tsakanin Faransa da Birtaniya kana ya dawo ƙasar [Nijeriya],” in ji sanarwar.
Daga bisani shugaban na Nijeriya ya tashi daga Abuja inda ya nufi Turai a jirgin shugaban ƙasa.
Tun da ya hau karagar mulki, shugaban Nijeriya ya yi tafiya-tafiye sosai.
A watan Oktoban shekarar 2024 ma shugaban na Nijeriya ya tafi hutun shekara-shekara na mako biyu.
A wancan lokacin, wata sanarwa da Onanuga ya fitar ta ce shugaban zai tafi Birtaniya ne domin yin hutun.
“Zai yi amfani da makonnin biyun ne a matsayin hutun aiki da kuma lokacin tunani game da garambawul ɗin tattalin arziin gwamnatinsa,” in ji sanarwar da Onanuga ya fitar a wancan lokacin.

















