Rasha na shirin gina tashar makamashin nukiliya a duniyar wata a cikin shekaru goma masu zuwa don samar da shirin sararin samaniya na wata da kuma haɗin gwiwar cibiyar bincike ta Rasha da China yayin da manyan ƙasashen biyu ke ƙoƙarin bincika tauraron ɗan’adam na duniya guda ɗaya tilo.
Tun lokacin da ɗan-sama-jannati na Soviet Yuri Gagarin ya zama ɗan’adam na farko da ya shiga sararin samaniya a shekarar 1961, Rasha na alfahari da zama babbar jagora wajen bincike da yawo a sararin samaniya, amma a 'yan shekarun nan ta kasance a bayan Amurka da kuma China da suke kara shiga duniyar ta sama.
Burin Rasha ya fuskanci babban koma-baya a watan Agustan 2023 lokacin da aikinta na Luna-25 mara matuƙi ya faɗo a kan duniyar wata yayin da yake ƙoƙarin sauka, kuma Elon Musk ya kawo sauyi ga ƙaddamar da motocin zuwa sararin samaniya - wanda a baya fanni ne na ƙwarewar Rasha.
Kamfanin binciken sararin samaniya na Rasha, Roscosmos a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa yana shirin gina tashar wutar lantarki a duniyar wata nan da shekarar 2036 kuma ya sanya hannu kan kwangila da kamfanin jiragen sama na Lavochkin Association don tabbatar da hakan.
Roscosmos ya ce manufar wannan tasha ita ce ta samar da wutar lantarki ga shirin duniyar wata na Rasha, wanda ya hada da na'urorin hangen nesa da kuma kayayyakin more rayuwa na hadin gwiwa tsakanin Rasha da China a fannin binciken sararin samaniya.
"Wannan aikin muhimmin mataki ne na ƙirƙirar tashar kimiyya mai aiki na dindindin da kuma sauya wa daga ayyukan bincike na lokaci ɗaya zuwa shirin bincike a duniyar wata na dogon lokaci," in ji Roscosmos.
Roscosmos bai bayyana karara cewa tashar za ta zama ta nukiliya ba, amma ya ce wadanda za su yi aikin sun haɗa da kamfanin nukiliya na ƙasar Rasha Rosatom da Cibiyar Kurchatov, babbar cibiyar bincike ta nukiliya ta Rasha.
Shugaban Roscosmos, Dmitry Bakanov, a watan Yuni ya bayyana cewa ɗaya daga cikin manufofin kamfanin shi ne samar da tashar wutar lantarki ta nukiliya a duniyar wata da kuma bincike a duniyar Venus, wanda aka sani da duniya "'yar'uwar" tamu duniyar.
Wata, wanda ke da nisan kilomita 384,400 daga duniyarmu, na daidaita motsawar duniya a kan ginshiƙinta, wanda ke tabbatar da yanayi mai kyau.













