Turkiyya ya yi Allah wadai da ta'addancin da mayaƙan Rundunar RSF ke yi wa fararen-hula a Sudan.
"Muna Allah wadai da ta'addancin da mayakan RSF na Sudan ke yi wa fararen-hula kuma muna kira da a gaggauta kai agajin jinƙai ga yankunan da abin ya shafa," in ji wakilin Turkiyya a Majalisar Ɗinkin Duniya Ahmet Yildiz a wani taron Kwamitin Tsaro na Majalisar kan Sudan a ranar Litinin.
Yildiz ya ce Sudan ta zama "mafi girman matsalar 'yan gudun hijira a duniya" kuma Ankara ta "yi matuƙar baƙin ciki" kan abubuwan da suka faru kwanan baya a Al Fasher da yankin Kordofan.
Ya kuma yi Allah wadai da harin da mayaƙan RSF suka kai a ranar 13 ga Disamba kan sansanin samar da kayayyaki na Rundunar Tsaron Wucin Gadi ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Abyei a Kadugli, Kudancin Kordofan, wanda ya kashe sojojin kiyaye zaman lafiya shida na Bangladesh tare da jikkata wasu takwas.
"Turkiyya ta amince da haɗin kan Sudan, darajar yankunanta, ikon mallaka da 'yancin kai a matsayin ɗaya daga cikin manyan manufofinmu na tsarin da ya dace da yankin da ma Afirka baki ɗaya," in ji Yildiz.
"Ta hanyar halacci da tattaunawa ne kawai za a iya samun mafita mai ɗorewa ga rikicin," in ji Yildiz, yana goyon bayan shirye-shiryen yanki da na duniya don kawo ƙarshen yakin.
"Ya kamata ƙoƙarin kasashen duniya ya zama tsarin zaman lafiya mai tafiya da kowanne bangare wanda zai bayar da damar tsagaita wuta na dindindin tare da cikakken tsarin siyasa da gaskiya," in ji shi.
Turkiyya na ci gaba da tuntubar Sudan
Da yake nuna ci gaba da huldar da ke tsakanin Turkiyya da Sudan, ya ce jiragen ruwan agaji na Turkiyya sun kai kusan tan 10,000 na taimako, yayin da aka aika da kayan kiwon lafiya don yaki da kwalara, kuma an aika da tantuna 30,000.
"Dole ne a 'yantar da mutanen Sudan daga hannun tashin hankali da mutuwa," Yildiz ya kara jaddadawa.
Tun watan Afrilun 2023 mayƙan RSF ke fafata rikici da sojojin Sudan.
A ranar 26 ga Oktoban wannan shekarar, sojojin RSF suka mamaye Al Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa, bayan wata kawanya ta kwanaki 500, wadda ta haifar da kisan gilla, korar mayaka, da kuma barin fararen hula a makale ba tare da samun abinci ba.



















