| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Libya ta sanar da zaman makoki na kwana uku bayan mutuwar Babban Hafsan Sojojin kasar
Babban Hafsan Sojojin Libya Mohammed al-Haddad da wasu manyan jami’ai hudu sun mutu a hatsarin jirgin kasa a kudancin Ankara, in ji jami’an gwamnatin Turkiyya.
Libya ta sanar da zaman makoki na kwana uku bayan mutuwar Babban Hafsan Sojojin kasar
Shugaban Majalisar Shugabancin Libya, Mohamed Menfi ya bayyana mutuwar a matsayin babban rashi ga sojojin Libya da al'ummar kasar. / AA
24 Disamba 2025

Libya ta ayyana kwanaki uku na zaman makoki na kasa bayan mutuwar Babban Hafsan Sojojin kasar Mohammed al-Haddad da manyan jami'an soji hudu a wani hatsarin jirgin sama kusa da babban birnin Turkiyya, Ankara.

A wata sanarwa a ranar Talata, Gwamnatin Hadin Kan Kasa ta Libya ta mika ta'aziyyarta ga iyalan wadanda suka mutu da kuma abokan aikinsu na Rundunar Sojin Libya.

A lokacin zaman makokin na kwanaki uku, za a yo kasa zuwa rabi da tutoci a dukkan cibiyoyin gwamnati da misalin karfe daya na yamma, yayin da za a dakatar da duk wasu taruka da bukukuwa na gwamnati, in ji sanarwar.

"Gwamnatin Hadin Kan Kasa tana mika ta'aziyyarta da kuma jaje ga iyalan wadanda suka mutu da kuma abokan aikinsu na rundunar," in ji sanarwar, tana mai addu'ar Allah ya ji kan wadanda suka mutu da kuma hakurtar da iyalansu.

Tun da fari, shugaban Majalisar Shugabancin Libya, Mohamed Menfi, ya fitar da sakon ta’aziyyar Babban Hafsan Sojojin Mohammed al-Haddad da manyan jami'an soji hudu da suka mutu a wani hatsarin jirgin sama kusa da babban birnin Turkiyya, Ankara.

A wata sanarwa da aka fitar a shafin X, Menfi ya bayyana mutuwar a matsayin "babban rashi ga rundunar sojin Libya da dukkan al'ummar kasar."

"Libya ta rasa shugabannin sojojin kasa wadanda suka sadaukar da rayukansu wajen yi wa kasar hidima, wadanda suka dauki ragamar sauke nauyin da ke kawunansu cikin aminci a cikin mawuyacin hali, kuma suka yi aikinsu da kyakkyawar ruhi ta ladabi, jajircewa da biyayya, suna sanya sha'awa, tsaro da kwanciyar hankali na kasar sama da duk abin da ake la'akari da shi," in ji shi.

Menfi ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda abin ya shafa da kuma sojojin kasar.

Ministan Harkokin Cikin Gida na Turkiyya, Ali Yerlikaya, a baya ya ce an gano buraguzan jirgin samfurin Falcon 50 da ke dauke da al-Haddad a kudancin garin Haymana, kusa da Ankara.