| Hausa
TURKIYYA
1 minti karatu
Shugaban Turkiyya ya yi wa Firaiministan Libya ta'aziyya kan mutuwar babban hafsan sojin ƙasar
Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya yi ta'aziyya ga Abdul Hamid Dbeibah ta wayar tarho bayan hatsarin jirgin sama a Ankara da ya kashe babban hafsan sojojin Libya, in ji daraktan sadarwa na Turkiyya.
Shugaban Turkiyya ya yi wa Firaiministan Libya ta'aziyya kan mutuwar babban hafsan sojin ƙasar
Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya yi wa Firaministan Libya Abdul Hamid Dbeibah ta’aziyya kan mutuwar babban hafasan sojojin kasar / AA
kwana ɗaya baya

Shugaban Turkiyya ya zanta ta wayar tarho da Firaiministan Libya, inda ya yi masa ta’aziyya kan hatsarin wani jirgin sama da ya yi sanadiyar mutuwar babban hafsan sojin Libya a Turkiyya, a cewar daraktan sadarwa na Turkiyya Burhanettin Duran.

A yayin zantawar da ya yi Abdul Hamid Dbeibah a ranar Laraba, Shugaba Recep Tayyip Erdogan "ya nuna bakin cikinsa tare da ta'aziyya kan asarar rayuka da aka yi a hatsarin jirgin da ke dauke da Shugaban hafasan sojojin Libya, Janar Mohammed Ali Al-Haddad, da sauran mutanen da suka yi masa rakiya,’’ in ji Duran.

Tun da farko dai Ministan Harkokin Cikin Gida na Turkiyya Ali Yerlikaya ya bayyana cewa an gano tarkacen jirgin ƙirar Falcon 50, wanda ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Esenboga na Ankara zuwa Tripoli a ranar Talata, an gano shi ne kimanin kilomita 2 kudu da Kesikkavak a yankin gundumar Haymana ta Ankara.

An gano wani baƙin akwati na jirgin da kuma na'urar tantance magana ta jirgin a safiyar ranar Laraba, in ji Yerlikaya.

Ƙazalika, an soma gudanar da bincike kan waɗannan na'urori don gano musabbabin hatsarin.

Bayan mutuwar, Gwamnatin Haɗin Kan Ƙasa ta Libya ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku a ƙasar.