AFIRKA
2 minti karatu
Tchiroma Bakary: Sojojin Kamaru sun yi wa jagoran 'yan adawar kasar rakiya zuwa wuri mai 'aminci'
Shugaban jam'iyyar gwamnati Issa Tchiroma Bakary ya ce 'yan sandan suna tabbatar da tsaro tana, bisa rahoton da ya wallafa a Facebook.
Tchiroma Bakary: Sojojin Kamaru sun yi wa jagoran 'yan adawar kasar rakiya zuwa wuri mai 'aminci'
Sai dai Tchiroma bai bayyana adadin sojojin da suka yi masa rakiyar ba. / Reuters
17 awanni baya

Shugaban adawa na Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, ya bayyana a ranar Jumma’a cewa sojojin da ke biyayya gare shi sun raka shi zuwa wani wuri mai tsaro domin kare lafiyarsa bayan zaben da ake takaddama a kansa.

Tchiroma ya kasance yana cikin gidansa a birnin Garoua da ke arewacin kasar tun bayan zaɓen shugaban kasa da aka gudanar a ranar 12 ga Oktoba, wanda ya yi iƙirarin cewa shi ne ya lashe zaɓen.

Sai dai Tchiroma bai bayyana adadin sojojin da suka yi masa rakiyar ba.

"Ina godiya ga sojojin da suka nuna kishin ƙasa ta hanyar raka ni zuwa wuri mai tsaro kuma a halin yanzu suna tabbatar da tsarona," in ji Tchiroma a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Tsaron ƙasar Afirkan ya ƙi yin tsokaci ga kamfanin dillancin labarai na Reuters game da wannan lamari.

Zanga-zangar tashin hankali

A ranar Litinin, Majalisar Kundin Tsarin Mulkin Kamaru ta ayyana Shugaba Paul Biya, wanda ke da shekaru 92 kuma shi ne shugaba mafi tsufa a duniya, a matsayin wanda ya lashe zaɓen, lamarin da ya haifar da zanga-zangar tashin hankali a birane da dama na kasar da ke samar da mai da koko.

Zaɓen da ake taƙaddama a kansa ya ƙara dagula al’amura a kasar, inda ake zargin jami’an tsaro da kashe aƙalla masu zanga-zanga 23 da kuma tsare fiye da mutum 500, a cewar wata ƙungiya ta al’umma.

A wani saƙo daban da ya wallafa a Facebook a ranar Jumma’a, Tchiroma ya yi kira da a dakatar da abubuwa a ƙasar na tsawon kwanaki uku daga ranar Litinin, inda ya buƙaci magoya bayansa su dakatar da duk wasu ayyuka kuma su zauna a gida domin nuna rashin amincewa da sakamakon zaɓen.

"An tsayar da abubuwa cik a ƙasa, domin duniya ta san cewa muna yin turjiya kuma ba za mu miƙa wuya ba," in ji Tchiroma a wani bidiyo.

"Mu rufe shagunanmu, mu dakatar da ayyukanmu, mu zauna a gida, cikin shiru, domin nuna hadin kai da kuma tunatar da wannan gwamnati cewa karfin tattalin arziki yana hannun jama’a."