Kamfanin Tsaron Turkiyya na ASELSAN, ya kafa wata rumfa a filin da ake gudanar da bikin Teknofest a Istanbul inda yake bayar da dama baƙi su fahimci yadda tsarin tsaron sararin samaniya na Steel Dome ke aiki domin kawar da duk wata barazanar hari ta sama.
An fara wannan babban taron fasaha da jiragen sama na kwanaki biyar na Teknofest a Istanbul a ranar Laraba.
An shirya wannan biki ne ta hanyar haɗin gwiwar Asusun Turkish Technology Team (T3) da Ma’aikatar Masana’antu da Fasaha ta Turkiyya.
A cikin wannan biki, ana gudanar da abubuwa daban-daban, daga gasar fasaha zuwa zuwa baje-kolin jiragen sama da marasa matuƙa da kuma wasan jiragen.
An kuma yi baje-kolin sassa daban-daban na tsarin Steel Dome a wurin bikin domin masu kallo,
Ta hanyar amfani da na’ura ta zamani ta hoto, masu ziyarar na iya ganin yadda Steel Dome ɗin ke bayar da kariya ko da an samu wata barazana.
Kamfanin Turkiyya ya yi gwajin TF6000
Kamfanin TUSAS Engine Industries (TEI) ya yi gwajin injin turbofan ɗinsa na TF6000, wanda aka tsara, sannan aka samar da shi a cikin gida.
Shugaban TEI, Mahmut Aksit, ya bayyana cewa an tsara injin ɗin ne domin jiragen sama marasa matuƙa kamar Anka 3 na Turkiyya.
Ya ƙara da cewa injin ɗin yana da tsarin afterburner na TF10000, wanda ke da ƙarfin tashi na 10,000 Ibf ko fiye da haka, kuma za a yi amfani da shi don manyan jiragen sama kamar Kizilelma na Turkiyya.
"Afterburner yana nufin wata salansa ce da ke bayan jirgi mai fitar da wuta. Tare da afterburner, muna ƙara ƙarfin injin TF6000 ɗinmu zuwa ƙarfin tashi na 10,000. Wannan kuma kusan daidai yake da ƙarfin dawakai," in ji shi.