‘Yan sanda a babban birnin Tanzaniya, Dar es Salaam, sun harba hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa daruruwan masu zanga-zanga a ranar Laraba yayin da kasar ta Gabashin Afirka ke gudanar da zabe.
Shugabar kasa Samia Suluhu Hassan mai shekaru 65, tana da babban rinjaye a wannan zaben, yayin da babban abokin hamayyarta, Tundu Lissu ke fuskantar shari'ar cin amanar kasa. An hana jam’iyyarsa ta Chadema shiga takara.
Kungiyar da ke lura da intanet, NetBlocks ta bayyana a wata sanarwa a X cewa an samu "katsewar intanet a fadin kasa."
Matasa sun fito kan tituna a Dar es Salaam suna kona wani caji ofis duk da yawan jami'an tsaro da aka jibge a birnin, inda aka ajiye tankokin soji a wurare masu mahimmanci, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.
Wata motar soja ta wuce ta cikin taron jama'a amma ba ta dauki wani mataki kan masu zanga-zangar ba, in ji rahoton.
Ba kasafai ake zanga-zanga a Tanzaniya ba, saboda tattalin arzikin kasar yana da karfi sosai, wanda ya karu da kashi 5.5 cikin 100 a bara, bisa ga bayanan Bankin Duniya, saboda karfin kasar a bangarorin noma, yawon shakatawa da ma'adinai.
Rahotanni sun ce fitowar masu kada kuri'a ta yi kasa a birnin, inda aka samu rumfunan zabe kusan babu mutane a safiyar ranar, kamar yadda 'yan jaridar AFP suka gani.
Shugabar kasa Samia Hassan ta hau kan mulki daga matsayin mataimakiyar shugaban kasa a shekarar 2021 bayan rasuwar wanda ya gabace ta, John Magufuli.









