AFIRKA
3 minti karatu
Fararen-hula 177,000 sun maƙale a Al Fasher na Sudan, yayin da RSF ke ci gaba da kisa - Likitoci
Kungiyar Likitoci ta Sudan ta ce kusan fararen hula 2,000 aka kashe cikin sa’o’i kaɗan bayan da ‘yan tawayen suka shiga birnin.
Fararen-hula 177,000 sun maƙale a Al Fasher na Sudan, yayin da RSF ke ci gaba da kisa - Likitoci
Kungiyar Likitocin Sudan ta yi kira ga al’ummar duniya da ƙungiyoyin jin kai su ɗauki nauyin su kuma su kare mutanen Sudan. / AA
12 awanni baya

Mutane kusan 177,000 sun maƙale a birnin Al Fasher, babban birnin Jihar Darfur ta Arewa, wadda dakarun RSF (Rapid Support Forces) suka ƙwace a ƙarshen mako, yayin da rahotanni suka bayyana kisan gilla da kisan ƙare-dangi da wannan ƙungiyar ke aiwatarwa.

Ƙungiyar Likitocin Sudan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba ta bayyana cewa, “RSF ta aikata mummunan kisan gilla kan fararen-hula marasa makami bisa ƙabilanci, a wani yunƙuri na kisan ƙare-dangi. Rahotanni daga tawagoginmu na filin daga sun nuna cewa adadin waɗanda aka kashe ya kai dubban mutane, duk da matsalolin sadarwa da rashin tsaro gaba ɗaya.”

Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa RSF ta aikata munanan laifuka da suka haɗa da “kisan gilla ba tare da shari’a ba, shiga gidaje da ƙarfi, cin zarafin mata, da tilasta wa mutane su haƙa kabarinsu sannan su binne kansu da ransu.”

Sanarwar ta ce, kusan fararen-hula 2,000 aka kashe cikin sa’o’i kaɗan bayan da ‘yan tawayen suka shiga birnin.

RSF ta ƙwace Al Fasher a ranar Lahadi bayan gumurzu mai tsanani da sojojin Sudan. Tun watan Mayun 2024, birnin yana ƙarƙashin mamayar wannan ƙungiya.

“An kashe mutane marasa laifi ta hanyar ƙone su da ransu, yayin da mutane 177,000 suka maƙale, kuma mafi yawansu ana zaton sun fuskanci kisan gilla,” in ji kungiyar.

Kimanin mutane 28,000 daga Sudan sun rasa matsugunansu cikin sa’o’i 48, inda 1,000 daga cikinsu suka isa garin Tawila a wannan jiha.

A cewar Hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM), fiye da mutane 36,000 sun tsere daga Al Fasher tsakanin 26 zuwa 29 ga Oktoba.

RSF ta ci gaba da kai hare-hare kan hanyoyin tserewa don hana fararen-hula isa wuraren tsaro, kuma “waɗanda suka yi ƙoƙarin tserewa da mota an ƙone su da ransu a cikin motocinsu.”

Likitoci sun tabbatar da rahotannin da wasu ƙungiyoyi na cikin gida suka bayar kan munanan laifukan RSF da suka shafi tsarin kiwon lafiya da ma’aikatan lafiya.

“A Asibitin Saudiyya da ke Al Fasher an shaida kisan gilla na fiye da marasa lafiya 450 da ke cikin asibitin, tare da tsofaffi kusan 1,200, waɗanda suka jikkata, da marasa lafiya a wuraren kula na da lafiya,” in ji sanarwar.

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), fiye da ma’aikatan lafiya da marasa lafiya 1,200 aka kashe, yayin da 416 suka jikkata a hare-hare 185 da aka tabbatar RSF ta kai tun farkon yaƙin a watan Afrilu 2023.

Kungiyar ta yi Allah wadai da “mummunan kisan gilla da kuma rusa ayyukan jinƙai baki ɗaya” a Al Fasher. Ta tabbatar da cewa “waɗannan ayyuka sun zama kisan ƙare-dangi, tsarkake ƙabilanci, da kuma manyan laifukan yaƙi, suna ƙara wa tarihin munanan ayyukan wannan ƙungiya a Darfur.”

Ta yi kira ga al’ummar duniya da ƙungiyoyin jinƙai su ɗauki nauyin su kuma su kare mutanen Sudan.

Sojojin gwamnati da RSF suna cikin yaƙin basasa tun watan Afrilu 2023. Wannan rikici ya kashe dubban mutane kuma ya raba fiye da mutane miliyan 15 da matsugunansu.