Ka taɓa tunanin yadda rayuwarka za ta kasance idan ka farka da safe wata rana ka tarar cewa intanet ta daina aiki?
Babu biyan kuɗi ta intanet, babu aika saƙonnin imel, babu shiga TikTok, Facebook ko Instagram, balle zuwa YouTube domin kallon bidiyo. Haka kuma, wataƙila ba za ka iya gudanar da wasu muhimman ayyukan yau da kullum ba.
Tambayar ita ce: Har zuwa wane mataki rayuwarka za ta iya tafiya yadda ya kamata ba tare da intanet ba?
Wannan tambaya na da muhimmanci idan aka yi la’akari da cewa kimanin mutane biliyan 6.3 ne ke amfani da intanet a faɗin duniya, adadin da ya kai kashi 76 cikin 100 na al’ummar duniya.
A yau, intanet ta zama wani muhimmin ɓangare na rayuwar bil’adama. Daga harkokin banki da kiwon lafiya zuwa ilimi, sadarwa da ayyukan gwamnati, kusan babu wani fanni da tsarin fasahar zamani bai yi tasiri a kansa ba.
A ƙarƙashin tekuna kuwa, akwai wayoyin sadarwa na musamman da aka shimfiɗa waɗanda ke ɗaukar kusan kashi 99 cikin 100 na zirga-zirgar bayanan intanet tsakanin ƙasashe. Waɗannan wayoyi ne ke haɗa nahiyoyi da kuma tabbatar da ci gaba da sadarwa tsakanin sassan duniya.
Saboda haka, idan waɗannan tsare-tsare suka samu matsala, illar ba za ta tsaya ga rashin iya shiga shafukan sada zumunta ba. Ana iya samun tsaiko wajen biyan kuɗi, soke tashin jirage da kuma katsewar wasu muhimman ayyuka da miliyoyin mutane ke dogaro da su.
Wa ke da iko da tsarin da muke dogaro da shi?
Wani abin lura shi ne, yawancin ayyukan fasahar zamani da muke amfani da su sun dogara ne da wasu ƙalilan daga cikin manyan kamfanonin duniya.
Kamfanoni uku kacal, wato Amazon Web Services, Microsoft Azure da Google Cloud, suna da kashi 61 cikin 100 na kasuwar samar da kayayyakin more rayuwar ajiyar bayanai a girgije ta duniya.
Wannan babban kaso da kamfanonin ke da shi ya sake haifar da tambayoyi kan yadda duniya ta dogara da wasu ƙalilan wajen gudanar da muhimman tsare-tsarenta na fasaha.
Haka kuma, yana tayar da tambayoyi kan ƙarfin da ƙasashe da kamfanoni ke da shi na tinkarar matsalolin tsarin sadarwa, da kuma waɗanda ke da iko a kan hanyoyin da ke haɗa duniya.
Za mu iya rayuwa ba tare da intanet ba?
Yayin da fasaha ke ƙara zama wani ɓangare na kusan dukkan ayyukan yau da kullum, tambayar ko mun dogara da ita fiye da kima na ƙara zama mai muhimmanci.
A Nijeriya ma, inda ake tunkarar manyan zaɓukan ƙasar, intanet na taka muhimmiyar rawa wajen samun labarai, bibiyar abubuwan da ke faruwa da kuma tattauna batutuwan da suka shafi siyasa da zamantakewa.
To, shin da gaske za ka iya shafe yini guda ba tare da amfani da intanet ba?
Ko kuma rayuwarka ta kai matakin da ba za ta iya tafiya yadda ya kamata ba idan babu intanet?














