AFIRKA
3 minti karatu
Ana fargabar dubban mutane na cikin 'mummunan hatsari' a birnin Al Fasher na Sudan da RSF ta ƙwace
Ƙungiyar likitoci ta MSF ta ce jama'a da dama na cikin masifa sakamakon akwai ɗumbin mutane da dakarun RSF suka hana tsallakawa zuwa wurare masu aminci domin tsira.
Ana fargabar dubban mutane na cikin 'mummunan hatsari' a birnin Al Fasher na Sudan da RSF ta ƙwace
Ana zargin RSF da kisan ƙabilanci a Al Fasher / Reuters
9 awanni baya

Ana fargabar dubban fararen hula sun makale sannan suna cikin mummunan haɗari a birnin Al Fasher na Sudan bayan birnin ya koma hannun dakarun RSF, in ji kungiyar likitoci ta MSF a ranar Asabar, yayin da ministan harkokin wajen Jamus ya bayyana halin da ake ciki a wurin a matsayin "yanayi mai ban tsoro."

Tun daga watan Afrilun 2023, dakarun RSF suka fara yaki da sojojin gwamnati, kuma a ranar Lahadi suka kwace Al Fasher, suka kori sojojin daga sansaninsu na karshe a Darfur bayan watanni 18 na kunci da hare-haren bama-bamai.

Tun bayan ƙwace birnin, an samu rahotannin kashe ɗumbin mutane, cin zarafin mata, hare-hare kan ma'aikatan agaji, fashi da garkuwa, yayin da hanyoyin sadarwa kusan suka katse baki ɗaya.

Waɗanda suka tsira daga Al Fasher da suka isa garin Tawila da ke kusa sun yi wa AFP ƙarin bayani game da kashe-kashe da yawa, harbe yara a gaban iyayensu, da kuma dukan fararen hula tare da kwace musu dukiyoyi yayin da suke gudu.

Dubban mutane sun makale

Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutane 65,000 sun tsere daga Al Fasher tun ranar Lahadi, amma dubban mutane har yanzu sun makale. Kusan mutane 260,000 ne suka kasance a birnin kafin harin karshe na RSF.

"Adadi mai yawa na mutane suna cikin mummunan haɗari kuma RSF da abokan aikinsu suna hana su tsira zuwa wurare masu aminci," in ji MSF.

Kungiyar ta ƙara da cewa mutane 5,000 kawai ne suka samu damar isa Tawila, wanda ke da nisan kilomita 70 daga yamma.

Adadin mutanen da suka isa Tawila "bai zo daidai da yadda ake tsammani ba inda rahotanni ke ƙara fito da yawan kashe-kashe," in ji shugaban sashen agajin gaggawa na MSF Michel Olivier Lacharite.

"Ina duk mutanen da suka tsira daga yunwa da tashin hankali a Al Fasher?" kamar yadda ya yi tambaya.

"Amsar da ta fi yiwuwa, duk da cewa tana da ban tsoro, ita ce ana kashe su, hana su tserewa, ko kuma ana farautar su yayin da suke kokarin tserewa."

Wasu shaidu sun shaida wa MSF cewa wata tawaga ta mutane 500, tare da sojojin gwamnati da dakarun hadin gwiwa, sun yi kokarin tserewa a ranar Lahadi, amma mafi yawansu an kashe su ko kuma an kama su ta hannun RSF da abokan aikinsu.

‘Yanayi mai ban tsoro’

Waɗanda suka tsira sun bayar da rahoton cewa ana raba mutane bisa jinsi, shekaru, ko kuma kabilarsu, kuma da yawa har yanzu ana tsare da su don neman kudin fansa.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce a ranar Juma’a adadin wadanda suka mutu sakamakon harin RSF a birnin na iya kaiwa daruruwa, yayin da abokan sojojin gwamnati suka zargi kungiyar da kashe fiye da fararen hula 2,000.

A wani taro da aka gudanar a Bahrain a ranar Asabar, Ministan Harkokin Wajen Jamus Johann Wadephul ya ce Sudan tana cikin "yanayi mai ban tsoro, babbar matsalar jin kai a duniya."

Ya kara da cewa RSF ta "yi alkawarin kare fararen hula kuma za a hukunta su kan wadannan ayyuka."

Da take magana a taron, Ministar Harkokin Wajen Birtaniya Yvette Cooper ta bayyana rahotannin cin zarafi da cewa "abin tsoro ne matuka."

RSF ta samo asali daga dakarun Janjaweed da aka zarga da kisan kare-dangi a Darfur shekaru ashirin da suka gabata kuma tana fuskantar zarge-zargen aikata laifukan yaki a wannan rikici na yanzu.

Amurka ta riga ta yanke hukunci cewa RSF ta aikata kisan kare-dangi a Darfur.