WASANNI
2 minti karatu
Yadda kwazon Yamal a filin wasa ya ragu saboda ciwon matsematsi
Barcelona na ci gaba da tararrabi kan lafiyar tauraron ɗan wasanta, Lamine Yamal, wanda ke fama da ciwon matsematsi tun watan Agusta.
Yadda kwazon Yamal a filin wasa ya ragu saboda ciwon matsematsi
Gabanin ciwon nasa, Lamine Yamal yana yin yanka 11.3 duk wasa, amma tun bayan fara ciwo sai adadin ya dawo 9.1. / Reuters
12 awanni baya

Bayanai daga Barcelona sun nuna yadda kuzari da ƙoƙarin Lamine Yamal ya ragu a wasannin da ya buga a baya-bayan nan, sakamakon ciwon matsematsi da ke damun sa.

Barcelona na ci gaba da tararrabi kan lafiyar tauraron ɗan wasanta, Lamine Yamal, wanda ke fama da ciwon matsematsi tun watan Agusta.

Ciwon ɗan wasan da ya ƙi warkewa, ya haifar da damuwa a tawagar Barca, ganin cewa an yi magani tsawon makonnin amma babu cikakken sauƙi.

Barca ta gayyato ƙwararrun likitoci don yin gwaji kan Yamal mai shekaru 18, don a tantance ko yana buƙatar a yi masa tiyata don magance matsalarsa.

Alƙaluma game da ƙwazon ɗan wasan sun nuna cewa ciwon da ke damunsa ya fara tasiri kan yanayin wasansa, da yadda yake aiki a fili.

Baya ga cewa ya je hutun jinya na makonni inda ya gaza buga wa Barca wasanni huɗu, masu nazarin yadda yake taka ƙwallo a fili sun fitar da ƙarin bayanai kan ƙoƙarinsa.

Gabanin ciwon nasa, Lamine Yamal yana yin yanka 11.3 duk wasa, amma tun bayan fara ciwo sai adadin ya dawo 9.1.

Buga ƙwallo da yake saitin raga ya ragu daga 6.6 zuwa 3.8 duk wasa, wanda ya janyo tallafin da yake bayarwa wajen cin ƙwallo ya ragu daga 1.33 zuwa 0.6 a wasa guda.