Hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya ta ce ta kama wasu 'yan ƙasar Mexico biyar bisa zargin gudanar da wani dakin sarrafa ƙwayar methamphetamine, a wani samame da hukumomi suka ce yana da alaƙa da ƙungiyoyin fataucin miyagun ƙwayoyi na Latin Amurka.
Hukumar NDLEA ta ce kamen, wanda aka yi a kudancin ƙasar a ranar 11 ga Nuwamba, shi ne samame na biyar da aka kai kan manyan wuraren sarrafa ƙwayar meth tun daga watan Mayu, kuma dukkan wuraren suna da alaƙa da 'yan Mexico.
Ana ƙara nuna damuwa kan yadda ƙungiyoyin fataucin miyagun ƙwayoyi na Latin Amurka ke ƙoƙarin kafa sansanoni a Nijeriya, ƙasa mafi yawan al'umma a Afirka, domin sarrafa ƙwayar methamphetamine da fitar da ita zuwa kasuwannin Turai da sauran wurare.
Hukumar ta ce ta kuma kama wani ɗan Nijeriya da ake zargin shi ne ya gina dakin sarrafa ƙwayar tare da taimaka wa 'yan Mexico biyar ɗin, waɗanda ta bayyana a matsayin ƙwararru kan sarrafa meth, da shiga ƙasar a watan Satumba ta hanyar amfani da fasfo na bogi.
Mai magana da yawun hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya ce jami'an hukumar sun ƙwato jimillar kilogiram 1,512 na ƙwayar methamphetamine, wadda aka riga aka sarrafa da kuma wadda ake kan sarrafawa, a masana'antar ta ɓoye.
Ya ce an kiyasta darajar ƙwayar da aka ƙwato ta kai dala miliyan 226.8.
Bincike na tsawon watanni bakwai
Babafemi ya kuma ce jami'an hukumar sun ƙwato tan da dama na wasu sinadarai da kayan aikin masana'antu da ake amfani da su wajen sarrafa ƙwayar meth.
Shugaban hukumar NDLEA, Mohamed Buba Marwa, ya ce an kama 'yan Mexico ɗin ne lokacin da jami'an hukumar suka kai samame a wurin da ake sarrafa ƙwayar a birnin Enugu, yayin da aka cafke ɗan Nijeriyan da ake zargi a wani otal da ke kusa da wurin.
Hukumar ta ce samamen ya biyo bayan binciken sirri na tsawon watanni bakwai, wanda ya bibiyi waɗanda ake zargin tun daga Mexico, ta Colombia da Faransa, har zuwa makwabciyar Nijeriya, Benin.
A yanzu haka, Nijeriya na tsare da 'yan ƙasar Mexico 10 bayan wannan samame na baya bayan nan. An kama biyar daga cikinsu a samamen da aka kai a baya, kuma tuni suke tsare yayin da ake jiran gurfanar da su a gaban kotu.













