Lokacin da sojoji suka kwace mulki a Guinea-Bissau a ranar 26 ga Nuwamba, kalmar da aka dinga amfani da ita a hukumance ita ce makircin da ya shafi "masu safarar miyagun kwayoyi" da kuma "amfani da makamai don canza tsarin mulki" ne ya tilasta wa sojojin tsoma hannu a harkokin mulki.
Tuni sojoji suka naɗa Janar Horta N'Tam a matsayin shugaban riƙon ƙwarya na ƙasar, wanda ya haifar da tsegumi game da lokacin da aka yi juyin mulkin da kuma zaɓen wanda ya zama shugaban riƙon ƙwarya.
Kwace mulkin soja ya zo ne a daidai lokacin da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ke shirin sanar da sakamakon zaɓen ranar 23 ga Nuwamba, inda Shugaba Umaro Sissoco Embaló ke neman zama shugaba na farko a cikin sama da shekaru ashirin da ya sami wa'adin mulki sama da saudaya kuma a jere a Guinea-Bissau.
Idan wannan bai isa ya zama abin cin karo da juna ba, mutumin da aka nada a matsayin shugaban riko wanda makusancin hambararren shugaban kasar ne ya dusashe hasken lokacin da ke tsakanin juyin mulkin da kuma manubar siyasa.
"Janar N'Tam yana da kusanci sosai da shugaban da aka hambarar, wanda kwanan nan ya naɗa shi a matsayin babban hafsan sojojin kasar. 'Yan adawa sun zarge shi da shiga cikin yakin neman zaɓen goyon bayan shugaban," in ji Amatijane Candé, wata 'yar jarida a Bissau, yayin tattaunawa da TRT Afrika.
"A gaskiya, duk mutanen da suka jagoranci juyin mulkin suna da kusanci da Shugaban, kuma sun shiga cikin yakin neman zaɓen da aka yi masa."
Babban ɗan takarar jam'iyyar adawa, Fernando Dias, ya yi zargin cewa kwace iko da sojoji suka yi wani "juyin mulki ne da aka ƙirƙira" daga wani Shugaba wanda "ba zai iya jure shan kaye ba".
Kalaman, waɗanda aka yi a wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, sun ƙara tayar da hankali kan ko wannan ƙasa ta Yammacin Afirka mai tarihi mai cike da rudani za ta fuskanci wani yanayi na rashin tabbas.
Sojoji sun ci gaba da kasancewa a kewayen fadar shugaban ƙasa a ranar Alhamis, ranar da hukumar zaɓe za ta sanar da sakamakon zaɓen.
Kasuwanci da bankuna sun kasance a rufe a faɗin babban birnin Bissau, inda yawancin mazauna birnin suka kasance a gidajensu.
Sojojin sun ce ana tsare da Embaló a hedikwatar rundunar soji kuma ana "ba shi kyakkyawar kulawa".
Hargitsin zabe
An yi tsammanin Embaló zai lashe zaɓen ne bayan da Kotun Koli ta ƙasar ta hana babban abokin hamayyar Shugaban ƙasar, Domingos Simoes Pereira yin takara, bisa dalilai na ayyuka.
Wannan zaɓen shi ne karo na farko a tarihin ƙasar da Jam'iyyar Afirka ta Pereira don 'Yancin Kai na Guinea da Cape Verde (PAIGC) ba ta bayyana a takadar zaɓen ba.
"Ina so kawai in sanar da ku cewa, mu ne aka yi wa wani yunƙurin juyin mulki na ƙarya. Ni ne wanda ya lashe zaɓen; ina da rahotannin cibiyoyin zaɓe da ke tabbatar da nasarata. Na yi nasara, to ta yaya zan iya shirya juyin mulki? Bayan haka, wa ke bayan wannan?" in ji ɗan takarar adawa Dias.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato Janar N'Tam yana cewa sojoji sun tattara shaidu "wadanda suka isa su ba da hujjar matakin da suka dauka", yana mai cewa "matakan da suka dauka na wajibi ne da ke bukatar gaggawa kuma suna da muhimmanci, sannan suna buƙatar saka hannun kowa".
Guinea-Bissau, ƙasa mai mutane miliyan 2.2, ta fuskanci juyin mulki da yunƙurin kwace iko tun bayan samun 'yancin kai daga Portugal sama da shekaru 50 da suka gabata. Kafin abubuwan da suka faru a wannan makon, yunƙurin juyin mulki na ƙarshe ya kasance a watan Oktoba.
"Mutane suna tunanin cewa wannan juyin mulki ne, ba ga Shugaban Ƙasa ba, sai dai ga sakamakon zaɓen," in ji Candé.
Martanin yankin
Ƙungiyar ECOWAS ta yankin ta yi gargaɗin cewa juyin mulkin ya ƙara barazana ga zaman lafiyar yankin da ya shaida yadda janar-janar na soja suka kwace iko a Guinea, Mali, Burkina Faso, Nijar da Gabon tun daga shekarar 2020.
"Abin sha'awa shi ne cewa a halin yanzu muna da aikin tallafa wa zaman lafiya na ECOWAS a ƙasar. Sun kasance a kasar fiye da shekaru uku, suna tabbatar da tsaro da amincin shugaban ƙasa da fararen hula," Candé ta fada wa TRT Afrika.
"Mutane suna jiran ganin irin rawar da ECOWAS za ta taka saboda ƙasar ta daɗe tana fuskantar irin wannan yanayi."
A ranar Laraba, Janar Denis N'Canha, shugaban ofishin sojojin fadar shugaban ƙasa, ya shaida wa manema labarai cewa sojoji sun karɓe iko da ƙasar "har sai an fitar da sanarwa ta gaba" kuma sun dakatar da "dukkan tsarin zaɓe".
Ya kuma sanar da dakatar da "dukkan shirye-shiryen kafofin watsa labarai" da kuma dokar hana fita waje.
A ranar Alhamis an sake bude iyakokin ƙasa, sama da na teku, waɗanda aka rufe bayan juyin mulkin, in ji Janar Lassana Mansali.
Mai magana da yawun Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya ce yana "bibiyar lamarin da damuwa sosai".
Shugaba Paul Kagame na Rwanda yana cikin waɗanda abubuwan da suka faru a Guinea-Bissau suka ruɗa tare da saka su a cikin damuwa.
"Lokacin da na fara jin labarin, na yi tunanin wani mutum na juyin mulki ga kan kansa," in ji shi, yana mai ƙara wa da cewa yana buƙatar lokaci don tabbatar da abinda ya faru.
Shugabannin ƙungiyoyin sa ido kan zaɓe sun yi kira ga Tarayyar Afirka da ECOWAS da su ɗauki duk matakan da suka dace don dawo da mulkin farar hula a kasar.













