| Hausa
WASANNI
3 minti karatu
Manchester United ta kori kocinta Ruben Amorim bayan ya soki shugabancin kungiyar
Sallamar da aka yi wa Amorim na zuwa ne ƙasa da awanni 24 bayan ya soki yanayin goyon bayan da yake samu daga kwamitin gudanarwa na United.
Manchester United ta kori kocinta Ruben Amorim bayan ya soki shugabancin kungiyar
Amorim mai shekaru 40, ya bar United ne watanni 14 bayan ka kama aiki. / Reuters
5 Janairu 2026

A ƙarshe dai kwanakin kocin Manchester United a ƙungiyar sun zo ƙarshe, bayan da shugabannin suka hukunta shi kan sukar da ya yi musu a ƙarshen makon jiya.

United ta sallami kocin nata ɗan asalin Portugal, watanni 14 bayan ka kama aiki, inda ya gaza farfaɗo da tagomashinta a kaka biyu da ya jagoranta.

Bayan wasansa na ƙarshe da United ta tashi 1-1 da Leeds, Amorim ya yi kakkausar suka ga shugabannin kwamitin gudanarwa na United.

Mai shekaru 40 a duniya, Amorim ya zo United ne a Nuwamban 2024, inda ya gaji Erik ten Hag. Ya jagoranci jimillar wasanni 63 inda ya ci 24 kacal, wato kashi 38 cikin ɗari.

Wata sanarwa da Man United ta fitar a shafinta na intanet ta ce, “Yayin da Manchester United ke mataki na shida a Gasar Firimiya, shugabannin kulob ɗin sun yanke hukunci cikin rashin son rai cewa lokaci ya yi na yin sauyi.

Wannan zai bai wa ƙungiyar kyakkyawar damar samun mafi kyawun mataki a Gasar Firimiya. Kulob ɗinmu na godiya ga Ruben saboda taimakonsa ga kulob ɗinmu kuma muna masa fatan alheri a gaba.”

Me Amorim ya faɗa

Sallamar da aka yi wa Amorim na zuwa ne ƙasa da awanni 24 bayan ya soki yanayin goyon bayan da yake samu daga kwamitin gudanarwa na United.

Ya faɗa wa ‘yan jarida bayan wasan da suka tashi da ci 1-1 da Leeds cewa yana fatan kai wa ƙarshen kwantiraginsa zuwa 2027 kafin ya tafi.

Ya ce, “Na zo nan don zama manajan Manchester United, ba na zama mai horarwa ba. Na san ba sunana Conte ba, Tuchel, ko Mourinho ba, amma ni manajan Manchester United ne. Haka za ta kasance nan da watanni 18 ko har lokacin da kwamiti za su yanke yin sauyi. Ba zan ajiye aiki ba. Zan yi aikina har sai wani ya zo gaje kujerata."

Ya ci gaba da cewa: “Kawai ina so na ce zan ci gaba da zama manajan wannan ƙungiya, ba wai koci kawai ba. Na faɗa ƙarara cewa a watanni 18 zan kammala sai kowa ya kama gabansa. Haka abin yake. Ba horarwa na zo yi ba.

“A kowane ɓangare, ɓangaren nemo ‘yanwasa, daraktan wasanni duka suna buƙatar yin aikinsu, zan yi aikina a watanni 18 sannan sai kowa ya kama gabansa.”

A halin yanzu Manchester United tana mataki na shida a teburin Gasar Firimiya da maki 31 daga wasa 20.

Cikin waɗanda ake ganin za su iya maye gurbin Ruben Amorim a United, akwai kocin Crystal Palace, Oliver Glasner, da tsohon tauraron Man United, Michael Carrick, da kuma tsohon kocin Chelsea, Enzo Maresca.