SIYASA
6 minti karatu
Yadda diflomasiyyar Erdogan na Turkiyya ta taimaka wajen cim ma tsagaita wuta a Gaza
A yayin da ake fargabar rushewar yarjeniyoyi, shigar Turkiyya cikin tattaunawar — da amfani da sanayya da dacewar ayyukan leƙen asiri — sun mayar da shawara mai rauni zuwa yarjejeniyar da ta haifar da sakamako mai ma'ana.
Yadda diflomasiyyar Erdogan na Turkiyya ta taimaka wajen cim ma tsagaita wuta a Gaza
Turkiyya na taka muhimmiyar rawa a siyasar Gabas ta Tsakiya kuma tana ta kokarin ganin an kawo karshen yakin Isra'ila a Gaza. / AA
6 awanni baya

A cikin wannan nasarar da aka zaci ba za ta yiwu ba akwai hannun Turkiyya dumu-dumu, wadda matsayinta mai shiga tsakani da garanto suka sauya komai na tattaunawar tsagaita wuta a Gaza.

Lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana shirinsa na samar da zaman lafiya a Gaza mai sharuɗɗa 20 a ranar 29 ga watan Satumba, an yi ta taka-tsantsan wajen mayar da martani.

Shirin ya yi alƙawarin kawo ƙarshen hare-hare, da musayar fursunoni, da taimakon jinƙai ba tare da cikas ba, amma ya bar babban giɓi.

Babu takamaiman hanyoyin aiwatar da shi, babu lokacin da za a janye, kuma babu wasu amintattun masu bayar da tabbacin tabbatar da aiki da yarjejeniyar.

Masu suka sun yi tambaya ko shirin ya fi zama kamar na wasan kwakwaiyon siyasa maimakon manufar da za iya cim ma wa. Da yawa sun yi nuni ga sanarwar ƙashin kai ɗaya tilo ta Trump da rashin tuntuɓar manyan masu shiga tsakani kamar Masar da Qatar.

Hamas, a nata ɓangaren, ta ce ba za ta yi la'akari da ƙwance ɗamara ko sakin fursunoni ba tare da ''lamunin garanto ba'' - wani jan layi da Turkiyya ta amince da shi daga baya saboda ta fahimci taimakawa sosai.

Yadda Turkiyya ta sauya wasan

An gayyaci Turkiyya don shiga tattaunawar da za a yi a Sharm El-Sheikh, wadda ke nuni da amincin Ankara da Hamas da kuma dangantakar Trump da Shugaba Erdogan na Turkiyya.

Shugaban tawagar Turkiyya shi ne shugaban Hukumar Leken Asiri ta Kasa (MIT) Ibrahim Kalin, wanda ke wakiltar diflomasiyyar siyasa ta Ankara, yana tuntuba da shirya yadda abubuw aza su tafi daidai.

 Ya taimaka wajen bayyana hangen nesa na Turkiyya na tsagaita wuta a lokacin da yake hada gana wa tsakanin Hamas, Amurka, Masar, da jami'an Qatar.

Sai dai kafin duk wadannan, abubuwan da suka kara taimaka wa su ne ziyarar da shugaba Recep Tayyip Erdogan ya yi a kai a kai da kuma samun nasara a ziyarar da ya kai Amurka, inda ya tattauna da shugaba Trump kan batutuwa masu muhimmanci, ciki har da batun Falasdinu.

A ranar Alhamis, Trump ya bayyana rawar da Erdogan ya taka wajen tabbatar da yarjejeniyar.

Masu sanya idanu kan tattaunawar ta Sharm El-Sheikh sun lura cewa shigar da Turkiyya ta yi ya taimaka wajen samar da ƙarin tsari da sahihanci ga tattaunawar da ta tsaya cak a baya.

Tattaunawar ta hada da tattaunawa game da tsarin ba da garantin bangarori hudu - wanda ya shafi Turkiyya, Masar, Qatar, da Amurka - don tabbatar da bin ka'ida, sa ido kan karya yarjejeniyar tsagaita wuta, da gudanar da musayar fursunoni.

Yayin da ake ci gaba da fayyace nauyi da alhakin da ke kan kowa, dabarun da aka yi aiki da su sun jaddada ƙoƙarin haɗin gwiwa don dorewar tsagaita wutar.

Wannan tsarin kai tsaye ya magance manyan bukatun Hamas: wanzuwar garanto ba wai a kyale Isra’ila ita kadai ba.

Har ila yau, tsarin ya bai wa Washington wata hanya ta siyasa don tabbatar da bangarorin da ke fada da juna. Shigar Ankara, duk da cewa an fara sa ido sosai a Tel Aviv, ya kasance ana kallon sa a matsayin muhimmi don tabbatar da Hamas ta bayar da haɗin kai.

Sakamakon haka, abin da ya fara a matsayin shawarwarin Amurka maras tabbas ya rikide zuwa wani tsari mai kyau, da ake saka wa ido, da kuma matakai. A cikin ‘yan kwanaki bayan Turkiyya ta shiga tattaunawar, bangarorin biyu sun amince da batun tsagaita wuta da dukkan manyan masu shiga tsakani za su baya.

Me ya sa wannan tsagaita wutar ya zama na daban

Wannan yarjejeniya ta bambanta da yunƙurin tsagaita wuta guda biyu da suka gabata - ɗaya a ƙarshen 2023 da kuma wata a farkon 2025 - waɗanda dukka biyun suka ruguje ƙarƙashin ci gaba da kai hare-hare ta sama daga Isra'ila, kuma saboda hanyoyin aiwatar da su ba su da ƙarfi ko ma babu su.

A wannan lokacin, tsarin ba da garanti daga ƙasashe da yawa - tare da ƙayyadaddun nauye-nauye, sanya idanu na ainihin lokaci, da kwamitin bin diddigi- sun samar da tsarin aiwatarwa wanda ba a gani a yarjejeniyoyin da suka gabata ba.

A ƙarkashin sabbin sharuɗɗan, musayar fursunoni da isar da agajin jinƙai za su kasance ne a jere. Ya kamata a kasafta makamai zuwa "masu kare kai" da "masu kai hari".

Ofishin siyasa na Hamas ya amince da yarjejeniyar.

A cikin makon nan ne dai aka kammala yarjejeniyar a birnin Sharm El-Sheikh. A cikin sa'o'i kaɗan, motocin dakon kayan agaji suka fara shiga Gaza ta kofar iyaka ta Rafah, wanda ke nuna kashin farko na aiki tsagaita wuta.

Saudiyya da Jordan, ko da yake ba masu shiga tsakani ba ne, sun shiga tattaunawar don ba da haƙƙin yanki da goyon bayan siyasa don dawo da tsaro da zaman lafiyar Gaza.

A wajen Turkiyya, wannan tsagaita wutar ta wuce nasarar diflomasiyya; wata dabara ce ta tabbatar da manufofinta na kasashen waje na dogon lokaci: cewa zaman lafiya mai dore wa a Gabas ta Tsakiya ya dogara ne da tsarin kafa kasashe biyu, tare da ingantaccen shugabanci a Falasdinu, adalci tsakanin bil'adama, da ingantaccen tsarin tsaro.

Shugaba Erdogan ya riga ya yi alƙawarin shigar Turkiyya cikin tawagar ta ƙasa da ƙasa da za ta sa ido kan aiwatarwa tare da gano mutanen Isra'ila da suka ɓace.

"In Allah ya yarda," in ji shi, "Turkiyya za ta shiga cikin rundunar da ke tabbatar da cewa yarjejeniyar ta ɗore."

Wannan tsagaita wutar ta riga ta sake fayyace rawar da Turkiyya ke taka wa a fannin diflomasiyya a yankin. Ƙarfinsa na yin hulɗa tare da abokan hulɗa na Yamma da Gabas ta Tsakiya ya inganta sunansa a matsayin amintaccen mai shiga tsakani, mai aiki, amintacce, kuma mai iya mayar da rikitattun manufofin siyasa zuwa shirye-shirye masu aiki.

Idan sulhun da aka yi a halin yanzu ya tabbata, zai zama shaidar cewa tabbataccen zaman lafiya yana buƙatar ra'ayin siyasa da kuma masu ba da tabbacin za a yi aiki da yarjejeniyar. Turkiyya ta bayar da duka.

A wajen Gaza, wannan a yanzu na nufin wata matsala mai rauni amma wadda ke bayar da damar haƙiƙa ta murmurewa, matuƙar dai hare-haren Isra'ila ya zo ƙarshe kuma dukka farfado wa, matukar dai an kawo ƙarshen hare-haren Isra’ila kuma kowanne ɓangare ya yi aiki da yarjejeniyar.

A wajen Turkiyya, wannan alama ce ta tabbatar da manufofin ƙasashen waje da tabbatar da kyawawan halaye tare da dabarun aiwatarwa, kuma ta sanya manufar kafa ƙasashe biyu a kan gaba. don samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.