Abin da ke faruwa a yau a Al Fasher, a kowace fuska, laifi ne ns cin zarafin bil'adama. Akwai shaidu masu karfi da ke nuna cewa RSF ta aikata manyan laifuka na take hakkin bil'adama kuma ta aikata ayyuka kai tsaye da suka saba wa dokokin yaƙi.
A cikin mako guda kacal, an kashe dubban mutane a gaban idanun duniya. Wannan, a kowace fuska, bala'i ne ga bil'adama.
Duk da haka, wannan ba shi ne karo na farko da Sudan ta shaida irin wannan bala’i ba. Tsawon watanni goma sha takwas da suka gabata, mutanen Al Fasher ke ƙarƙashin mamaya, suna mutuwa a hankali. Ba sa iya samun abinci.
A wani lokaci, an tilasta musu cin abincin dabbobi har ma da naman birai, beraye, da maguna. A wani kaulin, tun kafin kisan kiyashin na yau, an riga an fara wani salon kisan cikin jinkiri. A wannan matakin, yana da muhimmanci a fahimci irin tunani da yanayin tunanin da ke haifar da ta’addancin 'yan tawayen RSF.
Rugujewar adalci a duniya da matsayar Turkiyya
Turkiyya, tare da ƙasashe da dama da ke ƙaruwa, ta fara yin magana don nuna goyon baya ga al'ummar Sudan game da ta'asar da RSF ke yi.
Wannan yana nuna tsarin da Turkiyya ke bi wajen mayar da hankali kan manufofin ƙasashen waje.
A duk lokacin wani rikici a duniya, daga Sudan zuwa Gaza, muryar Turkiyya ta kasance mai ƙarfafa gwiwa da kuma bayyana halayya ta kwarai.
Dole ne a yarda cewa Shugaba Recep Tayyip Erdoğan yana cikin shugabannin duniya kaɗan da suka ci gaba da bayyana wa duniya irin mummunan halin jinkai da ake ciki a Sudan.
Abin takaici, wasu kaɗan ne suka yi irin haka. Majalisar Dinkin Duniya, a halin yanzu, ta sake gaza yin aiki yadda ya kamata.
Abin baƙin ciki, duniya ta saba da irin wannan gurguwar fahimta. Tambayar gaskiya ba ita ce ko ƙasashen duniya za su iya shiga tsakani ba, a’a shin suna son yin hakan.
Tsarin da duniya ke tafiya a kai yau ba ya samar da mafita ko yin adalci. An ga haka a Gaza, kafin sannan an gani a Bosnia da Rwanda. A yanzu ana sake shaida hakan a Sudan.
Rashin ɗaukar matakan ladabtarwa kan laifukan yaƙi da Firamiinistan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya aikata a Gaza na iya zama mafi bayyananniyar alamar wannan lalacewa. Amincewar jama'a ga tsarin shari'a na duniya ta rushe.
Babu wani matakin dakatar da waɗanda suke aikata ta'asa. Kowace rugujewar al’umma ta fara ne da lalacewar halayya, kuma tsarin duniya a yau yana tafiya a kan hakan.
Muhimmancin El-Fasher da darussan da aka yi watsi da su
El-Fasher yna da matuƙar muhimmanci. Idan kuka kalli taswira za kua shaida yana ya nuna garin a matsayin babbar hanyar shiga cibiyar hhada-hada da safarar kayayyaku., musamman a yanzun sa uke yaki ‘ya’addar RSF.
Duk da haka, yana da mahimmanci a lura cewa manyan yankunan Darfur masu arzikin zinare suna cikin Jebel Amir da Songo.
Muhimmancin Al Fasher ba ya dogara ne akan albarkatunta ba, amma yana matsayin mahaɗar gabas da yamma na Sudan.
Haka kuma yana da filin jirgin sama wanda ke da mahimmanci wajen gudanar da ayyuka.
Darfur ya ƙunshi manyan birane biyar. Al Fasher ne babban birnin Arewacin Darfur. Har zuwa makon da ya gabata, shi ne kawai birnin Darfur da ke ƙarƙashin ikon sojoji yayin da RSF sun riga sun mamaye Kudu, Yamma, Tsakiya, da Gabashin Darfur.
Bayan kawanya da aka yi ta tsawon shekara ɗaya da rabi, RSF ta karɓe iko da Al Fasher, ta mayar da dukkan Darfur ƙarƙashin ikonta. Saboda haka, faɗuwar birnin ba wai kawai alama ce ba; wani sauyi ne na siyasa.
A lokaci guda, abin da ake gani a Al Fasher ba komai ba ne illa karar da wata kabila. Akwai ƙa'idodin yaƙi amma mayakan RSF sun yi watsi da su. Shiga tsakani nan take na ƙasashen duniya yana da mahimmanci.
Hotunan tauraron ɗan adam sun nuna kaburbura da kisan gilla da yawa. Hana samun ƙarin ta'addanci da kare haƙƙin ɗan adam sun zama dole ne yanzu kuma ya kamata su zama babban fifikon kasashen duniya.
Zuwa yanzu, dukkan alamu sun nuna cewa RSF za ta ci gaba da karya dokokin jinkai na duniya da kuma ƙa'idodin rayuwar ɗan adam.
Misali, rahotanni sun nuna cewa wani shugaban 'yan bindiga da ake kira da "Abu Lulu" ya kashe tare da bayar da umarnin kashe fararen hula marasa adadi. Wannan lamari ne guda ɗaya kawai a tsakanin mutane da yawa. Babban batun shi ne rashin takunkumi mai tasiri.
Bayan ayyukan Isra'ila a Gaza, rashin aikin "dokokin kasa da kasa" ya bayyana fiye da kowane lokaci.
Ƙungiyoyi kamar RSF suna samun ƙarfin gwiwa daga wannan rashin bin doka domin ba sa yin aiki su kaɗai. Rahotanni da yawa, ciki har da waɗanda Majalisar Dinkin Duniya ta bayar, sun bayyana goyon bayan da suke samu daga kasashen waje.
A yau, ana shaida wata Gaza, amma a wannan karon a Sudan, a Al Fasher. Inda ake da irin dauin gindin da Isra'ila ke da shi, dokar ƙasa ta ruguje. A wannan lokacin, tsammanin bin dokokin yaƙi ko girmama haƙƙin ɗan adam ya zama mafarki.
Abin da ke faruwa a Al Fasher a yau shi ne ɗan adam yana shigar da kansa kara gaba shari’a. Kuma a cikin wannan shari'ar, wanda ake tuhuma ba wai kawai RSF ba ne, har ma da tsarin duniya da ya yi shiru yana kallo ba tare da yin komai ba.
Marubucin, Tunç Demirtaş malami ne a sashen Hulɗar Ƙasashen Duniya a Jami'ar Mersin, Turkiyya.
Togaciya: Ba lallai ra’ayin da marubucin ya bayyana ya zama ya yi daidai da ra’ayin dab’i na TRT Afrika ba.



















