Ɗan takarar shugaban Nijeriya na Jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023 kuma tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga shugaban Amurka Donald Trump da ya taimaka wa gwamnatin Nijeriya wajen tunkarar matsalar tsaron ƙasar maimakon barazanar kai hari a ƙasar.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi, Kwankwaso ya ce ya kamata gwamnatin Nijeriya ta ware wasu jami’an diflomasiyya domin tattaunawa da gwamnatin Amurka.
Kalaman na Kwankwaso na zuwa ne bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana Nijeriya cikin ƙasashe da Amurka take sanya wa indo game da zargin kisan Kiristoci da kuma barazanar kai hari Nijeriya idan gwamnatin ƙasar ba ta hana kashe Kiristoci ba.
“Yana da muhimmanci in jaddada cewa ƙsarmu ƙasa ce mai cin gashin kanta wadda mutanen suke fuskantar barazana daga ɓata gari a faɗin ƙasar. Rashin tsaron da muke fuskanta ba ya bambantawa bisa adinim ƙabila ko aƙidar siyasa,” a cewar Kwankwaso.
“Ya kamata Amurka ta taimaka wa hukumomin Nijeriya da ingantattun fasaha domin daƙile matsalolin, maimakon yin barazanar da za ta daɗa raba ƙasarmu,” in ji Kwankwaso.
Baya ga haka Kwankwaso ya shawarci gwamnatin Nijeriya ta tura jam’in diflomasiyya na musamman domin tattaunawa da gwamnatin Amurka.
“Bugu da ƙari, yana da muhimmanci a naɗa jakadu na dindindin domin wakiltar manufofin Nijeriya a a duniya,” a cewar tsohon gwamnan na jihar kano.
“Ga ‘yan uwana ‘yan Nijeriya, wannan wani muhimmin lokaci ne inda ya kamata mu bai haɗin kai fifiko maimakon rarrabuwar kai,” in ji shi.










