Gwamnatin Amurka na yunƙurin hana bayar da biza ga mutane masu kiba da masu ciwon sukari, da kuma yara masu buƙata ta musamman.
Wannan shi ne sabon matakin da Shugaba Donald Trump ya ɗauka don ƙin yarda da baƙin-haure a matsayin wani ɓangare na matakansa na taƙaita shige da fice.
A cikin wata wasiƙa da aka aiko a farkon wannan wata, Sakataren Harkokin Waje Marco Rubio ya bukaci ofisoshin jakadancin Amurka a duniya su yi la'akari da yanayin lafiya wajen bayar da biza na dogon lokaci, kamar yadda kafafen watsa labarai na Amurka suka ruwaito.
A cikin wasiƙar, wadda KFF Health News ta fara ruwaitowa, Rubio ya ce kasancewa mai kiba, mai ciwon sukari, ko mai nakasa na iya "buƙatar kulawa mai tsada, na dogon lokaci," wanda ka iya zama nauyi ga kuɗaɗen gwamnati.
Sabbin ƙa'idodin sun fi mayar da hankali kan mutane da ke wajen Amurka ko waɗanda ke neman sabunta bizarsu.
Duk da haka, wasu ƙwararru sun yi gargaɗi cewa waɗannan ƙa'idojin na iya shafar iyalan mutanen da tuni suke zaune a Amurka waɗanda suke so su je kai ziyara.
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), a 2022, fiye da mutum biliyan 1 ke rayuwa da kiba, inda alƙaluman suka danganci abinci da rashin motsa jiki.
Amurka tuni tana ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi yawan masu ƙiba a duniya, kimanin kashi 40% na al'ummarta na da kiba.
Sabbin ƙa'idojin sun haɗa da hana ko soke biza ga mutane da ke adawa da manufofin wajen Amurka, ciki har da maganganun da suka yi kan Isra'ila, wadda ake zargi da ɗaukar wani yaki na kisan ƙare-dangi kan 'yan Falasdinu.
Ba a fayyace lokacin da sabon manufofin za su fara aiki ba.
Gwamnatin Trump ta kasance tana ƙoƙarin hana masu gudun hijira shiga Amurka, tare da aiwatar da korar baki, har da mayarwa zuwa Afirka.
Ta saka haramcin biza ko ƙa'idoji masu tsauri kan wasu ƙasashen Afirka.
















