AFIRKA
2 minti karatu
Shin El-Fasher da ke ƙarƙashin ƙawanyar RSF a Sudan za ta zama tamkar Gaza?
Fararen hula 300,000 sun shafe kusan kwanaki 500 suna a maƙale yayin da aka tilasta wa sama da mutum 780,000 barin gidajensu.
Shin El-Fasher da ke ƙarƙashin ƙawanyar RSF a Sudan za ta zama tamkar Gaza?
Kimanin fararen hula 300,000 aka raba da duniya tun wajen shekara ɗaya da ya gabata ciki har da ƙananan yara 130,000. / TRT World
7 awanni baya

Tun watan Afrilun shekarar 2024, birnin El-Fasher, babban birnin jihar North Darfur, ya yi fama da bala’in ƙawanya na rundunar RSF.

Fararen hula kimanin 300,000 sun shafe kimanin kwanaki 500 a maƙale yayin da aka tilasta wa sama da mutum 780,000 barin gidajensu.

An hana su samun abinci da ruwa da kiwon lafiya. Rashin abinci mai gina jiki a tsakanin ƙananan yara yana ƙaruwa zuwa wani mataki mai tayar da hankali, kuma an tilasta wa iyalai su yi rayuwa kan “Elumbaz”—wadda ake samowa daga irin auduga da gyaɗa da ake amfani da su wajen abincin dabbobi.

El-Fasher shi ne muhimmin birni na ƙarshe da ke hannun gwamnati a jihar North Darfur, kuma hare-haren rundunar RSF sun lalata sansanin ‘yan gudun hijira na Abu Shouk, inda suke kai hare-hare kan kasuwanni da ababen more rayuwa da dararen hula ta hare-haren jirage mara matuƙa da manyan bindigogi.

Maƙale a sansanoni

Rahotannin MDD a hukumance sun ce fararen hula 300,000 mara makamai an yanke su daga sauran duniya sama da shekara ɗaya da ya wuce, ciki har da yara 130,000 a sansanonin ‘yan gudun hijira na Abu Shouk da Zamzam.

Hukumar samar da abinci ta duniya ba ta samu damar ba da abinci ba tun farkon shekarar 2024, kuma zuwa watan Maris ɗin shekarar 2025, kashi 38 cikin 100 na yara ‘yan ƙsa da shekara biyar suna fama da rashin abinci mai gina jiki.

Sakamakon na da muni. Tsakanin watan Afrilun shekarar 2023 da watan Julin shekarar 2025, kusa mutane 782,000 ne suka tsere daga El-Fasher, inda yankin Tawila ya karɓi baƙuncin kashi uku cikin huɗunsu.

Duk da haka sama da fararen hula 180,000 sun maƙale a sansanin Zamzam, inda suke fuskantar barazanar kisan kiyashi idan suka yi ƙoƙarin barin wurin.

An naɗi bidiyon rundunar RSF inda suke gana wa mutane azaba kuma aka wallafa hoton bidiyon a kafafen sada zumunta, lamarin da ya nuna yadda suke cin karensu babu babbaka.

Matslaar jinƙan na da tsanani sosai. An lalata asibitoci 35 da makaranti shida.

Wuraren ajiyar jini da wuraren gwaje-gwaje da asibitoci sun daina aiki sakamakon luguden wutan rundunar RSF da kuma ƙarancin abubuwa masu muhimmanci.

Fannin ilini da kiwon lafiya sun durƙushe gabaɗaya. Idan ƙawanyar ya cigaba, dole a samu yunwa a cikin ƙananan yara.