| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
RSF na rushe hujjoji kan ta'asar da ta faru a Sudan: Rahoto
Kungiyar 'yantawaye ta RSF ta Sudan ta gudanar da kashe-kashe da yawa da kuma zubar da gawarwaki barkatai a birnin Al Fasher, kamar yadda wani sabon rahoto ya gano.
RSF na rushe hujjoji kan ta'asar da ta faru a Sudan: Rahoto
RSF na rushe hujjoji kan ta'asar da ta faru a Sudan: Rahoto / User Upload
19 awanni baya

Wani sabon rahoto ya gano cewa ƙungiyar ‘yantawaye ta "Rapid Support Forces" (RSF) ta Sudan ta yi kashe mutane da dama tare da watsar da gawarwakinsu a birnin Al Fasher.

Dakin Binciken Jinƙai na Jami'ar Yale (HRL), wanda ya yi amfani da hotunan tauraron ɗan’adam don sa ido kan azabtarwa tun bayan barkewar yakin RSF da sojojin ƙasar, a ranar Talata ya ce ƙungiyar "ta ruguza kuma ta ɓoye hujjojin yawaitar kisan gilla da ta aikata" a babban birnin Jihar North Darfur.

Mamayar tashin hankali ta RSF ta karɓi waje na ƙarshe da sojoji ke riƙe da shi a yankin Darfur a watan Oktoba, wanda ya haifar da ƙiyayya a duniya bisa rahotannin kisan gaggawa, da fyade da kamun jama'a da yawa.

HRL ya ce a bayan mamayar, ya gano abubuwa 150 da suka gi kama da ragowar jikin ɗan’adam.

Ba su dace da hanyoyin binne fararen hula ba

Gommai sun yi daidai da rahotannin kisan gilla, da kuma wasu da dama da rahotannin RSF na kashe fararen hula yayin da suke guduwa

A cikin wata guda, ba a sake ganin kusan 60 daga cikin waɗannan abubuwa masu kama da jikkuna ba, yayin da aka ga ramuka takwas ko wasu alamomi a ƙasa kusa da wuraren da aka yi kashe-kashen, in ji HRL.

Ya ce waɗannan ramukan ko alamomin ba su dace da yadda fararen hula ke binne mamaci ba.

Rahoton ya ƙaddara cewa "an yi kisan mutane da yawa ta tsarin sannan an ɓoye gawawwaki", yana kiyasta cewa adadin waɗanda aka kashe a birnin nya kai dubbai.

Yaki mai muni

Kungiyoyin agaji da Majalisar Dinkin Duniya sun ci gaba da neman izinin shiga cikin Al Fasher cikin aminci, inda sadarwa ke yankewa kuma ana kiyasta cewa dubban mutane sun makale, da yawa kuma suna tsare a hannun RSF.

Babu adadin yawan waɗanda suka mutu a hukumance daga yakin Sudan, wanda ya fara a watan Afrilun 2023; amma ana kiyasta mutuwar fiye da 40,000.

Shugaban Kwamitin Mulkin Wucin Gadi na Sudan, Janar Abdel Fattah al‑Burhan, shi ne ke jagorantar sojoji, yayin da RSF ke karkashin jagorancin tsohon mataimakinsa, Mohamed Hamdan Dagalo.

Fadan ya kuma tilasta wa miliyoyin mutane gudun hijira, tare da haifar da mafi girman rikicin yunwa da ƙaura a duniya.