Rundunar ‘yansandan Jihar Neja a arewa ta tsakiyar Nijeriya ta ce ta kama mutum shida bisa zargin aikata laifukan da suka haɗa da safarar makamai da garkuwa da mutane da ƙwacen waya.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Wasiu Abiodun, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, yana mai cewa an kama waɗanda ake zargin ne a samamen da aka kai wurare daban-daban a faɗin jihar.
Ya ce jami’an rundunar ‘yansandan da suka yi aiki da bayanan sirri game da wata mai suna Zuwaira Usman wadda aka ce ta ƙware a safarar makamai wa ɓata-gari, sun kama wadda ake zargin ranar 4 ga watan Nuwamban shekarar 2025.
Ya bayyana cewa wadda ake zargin ta amsa cewa ta haɗu da wani mai suna Lawali a Birnin-Gwari, da ke Jihar Kaduna a watan Satumbar shekarar 2025 inda suka yi musayar lambobin waya. A cikin tattaunawarsu, ta ce Lawali ya nemi ta je ta karɓo masa saƙo daga Warri, Jihar Delta.
“Ta yi iƙirarin cewa Lawali ya ba ta naira N20,000 a matsayin kuɗin mota, inda ta yi tafiyar. Da ta isa Abuja, ta bayyana cewa Lawali ya yi magana da direban kuma ya sanar da shi inda za a sauke ta a Warri.
“Zuwaira ta ƙara bayyana cewa da ta isa inda za ta je, ta haɗu da wani mutum kan babur wanda ya ba ta wani buhu da aka saka filas wanda ke ɗauke da wasu abubuwa domin ta kai wa Lawali. Ta ce mutumin, wanda daga baya aka bayyana sunansa a matsayin Ahmed, ya kuma ba ta ƙarin kuɗi N30,000 domin tafiyarta zuwa Kaduna.
“Ta koma da Abuja, sa’annan Jihar Kaduna da kayan, inda ta miƙa wannan buhun ga Lawali a Birnin-Gwari. Daga baya ne aka gane cewa filas din na ɗauke da harshasai 2,500 na bindigar AK-47.
“Ƙarin bayani ya nuna cewa daga baya an kama Ahmed a Jihar Delta, yayin da ake ƙoƙarin kama Lawali inda ake ci gaba bincike,” in ji jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yansandan Jihar ta Neja.
Abiodun ya ƙara da cewa ranar 27 ga watan Nuwamba, ma’aikata sun kama wani mai suna Aminu Ahmed bisa zargin garkuwa da yara uku a Kontagora da kuma karɓar kuɗin fansa da ya zarce naira miliyan biyu.
Ya bayyana cewa wanda ake zargin ya amsa laifin garkuwa da wani yaro mai shekara uku da kuma karɓar naira miliyan 1.4 a matsayin kuɗin fansa kafin ya sake shi. An kuma ce ya amsa garkuwa da wani yaro ɗan shekara huɗu da kuma wani mai shekara uku a cikin Kontagora, inda ya karɓi kuɗin fansa da ya kai naira N850,000 kafin ya sake su.
“Ya kuma yi iƙirarin cewa an yi masa damfarar kuɗin da ya kai naira miliyan 1.8 a wata harkar haƙar ma’aidinai. Ana ƙarin bincike a kan wanda ake zargin,” in ji Abiodun.
Jami’in hulɗa da jama’an ya ƙara da bayyana cewa wani samamen da aka kai ranar 30 ga watan Nuwamba ya sa an kama wani mai suna Mohammed Mahmud da ke Zuba, wanda aka samu da wata bindiga da aka ƙera a gida da ke da harsashi ɗaya a lokacin caji.
A wani samamen kuma, Abiodun ya ce, “ranar 10 ga watan Disamba na shekarar 2025, da misalin ƙarfi 4:30, ‘yansintirin rundunar ‘yansanda na Operation Flush da ke ofishin ‘yansanda na Chanchaga sun kama mutum biyu da ake zargi—Hassan Abdullahi, mai shekara 19, da ke unguwar Mandela, da Khalifa Bashir, mai shekara 21, a Bosso.
“Waɗanda ake zargin an kama su ne a cikin a-daidaita-sahu a Old City Gate, kuma a lokacin bincike an same su da wayoyi ƙirar Android uku da ake zargin cewa sun sato su ne. Da ake musu tambayoyi, sun amsa cewa sun ƙwace wayoyin ne daga fasinjojin a-daidaita-sahun.”
Ya ƙara da cewa ranar 12 ga watan Disamba, rundunar ‘yansandan ta samu wani rahoton cewa wasu da ake zargi da kasancewa ‘yanfashi da makami suna kusa da dutsen Zuma.
Wannan, a cewar Abiodun, ya sa nan-take an tura ‘yansanda wurin, inda aka ƙwace bindigogi biyu da aka ƙera kuma aka ɗaure su da baƙin salatif.
Abiodun ya ƙara da cewa a ranar, an kama mutum biyu da ake zargi, Adamu Usman da Umar Mohammed Bello, a Kagarko bisa wani fashi da makamai da aka yi ranar 1 ga watan Nuwamba.
“A cikin bincike, an bi sawun ɗaya daga cikin wayoyin da aka sace zuwa ga mutanen da ake zargin a Kagarko. A lokacin da ake [musu] tambayoyi, sun amsa aikata laifin kuma sun ambaci sunayen sauran ‘yandaban.
“A halin yanzu dai waɗanda ake zargin suna taimaka wa binciken ‘yansanda yayin da ake ƙoƙarin kama ragowan ‘yandabar.
“An kuma kama wani Zakariyau Mohammed na unguwar Jubilee , da ke Suleja, ranar 11 ga watan Disamba na shekarar 2025, bisa haɗin baki da kuma satar kayayyakin gida.
“Bayanai sun nuna cewa wanda ake zargin ya haɗa baki ne da wani ami suna Aminu Na’wushe wajen satar kayayyakin, waɗanda suka haɗa da janareto da wasu sauran kayayykin lataroni daga wani gida a kan hanyar Kaduna . Ma’aikatan ‘ya sanda sun cafke Zakariyau da wuri kuma suka ƙwace kayayyakin, yayin da aka matsa kaimi wajen ƙoƙarin kama Aminu,” in ji Abiodun .















