‘Mummunan yanayi’: Duba ga tsarin kula da lafiya na Sudan da ke taɓarɓarewa
AFIRKA
10 minti karatu
‘Mummunan yanayi’: Duba ga tsarin kula da lafiya na Sudan da ke taɓarɓarewaSudan na fuskantar matsanancin rushewar tsarin kula da lafiya a yayinda aka rusa asibitoci, aka rufe hanyoyin kai kayan agaji da kuma yaɗuwar cututtuka.
A cewar UNICEF, an sami rahoton kamuwa da cutar kwalara sama da 7,700 da mace-mace 185 a Jihar Khartoum tun farkon 2025 / Anadolu Agency
2 awanni baya

Sudan na fuskantar matsalar jinƙai mafi girma a duniya, inda sama da mutane miliyan 13 suka rasa matsugunansu, yayin da dubbai suka rasa rayukansu.

Abin da ya fara a matsayin rikicin siyasa da na soja tsakanin Rundunar Sojojin Sudan da Rundunar Sojojin Sa Kai (RSF) a watan Afrilun 2023, ya rikiɗe zuwa wani babban rikici da ya rusa tsarin kula da lafiyar jama'a, da ayyukan yau da kullum, da kayayyakin more rayuwa na likitanci da tsaron fararen hula.

Yanayin kula da lafiya a Sudan ya taɓarɓare tare da zama "mummunan yanayi," inda wasu yankuna ke fuskantar gazawar tsarin gaba daya, in ji Dr Tunc Demirtas, mai bincike a yankin Kusurwar Afirka kuma malami a Sashen Hulɗar Ƙasashen Duniya a Jami'ar Mersin, yayin tattaunawa da TRT World.

Mahukuntan Sudan sun ce ko dai an lalata asibitoci, an kwashe kowa daga cikin su, ko kuma ana aiki a cikinsu a ƙarƙashin matsin lamba a Al Fasher, babban birnin Arewacin Darfur kuma yankin da aka yi kisan kiyashi da RSF ta jagoranta kwanan nan.

"Asibitin Turkiyya da ke Nyala ya kasance ɗaya daga cikin ƙananan cibiyoyin da ke aiki a yankin, duk da haka yana ƙara fuskantar ƙalubale saboda ƙarancin magunguna, da allurar kashe raɗaɗi da sa barci, da makamashi da muhimman kayayyaki," in ji Demirtas.

"Hanyoyin shige da fice ba su da aminci ko kuma an rufe su baki ɗaya, wanda hakan ya sa kusan ba zai yiwu ga fararen hula ba, musamman marasa lafiya da suka ji rauni, da mata masu juna biyu da yara, su isa wurin kula da lafiya ba," kamar yadda ɗan jarida Mohammed Nazar Awad, mai shekaru 25, ya faɗa wa TRT World.

Demirtas ya jaddada cewa ƙuntatawar RSF, tashin hankali da kuma toshe hanyoyin isar da kayan agaji sun bar fararen hula ba tare da ruwan sha mai tsafta, da rashin kayan tsafta, ko kuma isasshen damar samun abinci ba.

Rushewar tsarin kula da lafiya

A cewar Ma'aikatar Lafiya ta Sudan, cikin shekara ɗaya da rabi da ta gabata, rufe hanyoyin ya haifar da ɓarkewar cutar kwalara, cutar mashaƙo ta diphtheria, da cizon sauro, da typhoid da zazzabin dengue, yayin da rashin abinci mai gina jiki ya ƙara ta'azzara yanayin waɗannan cututtuka. Tasirin da ya haifar shi ne durƙushewar tsarin kula da lafiya a matakin ƙasa.

Tsananin rikicin ya ƙara bayyana a cikin shaidar Dr Tijani Muhammad Hassan, wani mai ba da shawara kan lafiyar ƙwakwalwa kuma mataimakin farfesa wanda ya yi aiki a tsarin kiwon lafiya na Sudan tun daga shekarar 2006.

Ya shaida wa TRT World cewa yaƙin ya kasance abin takaici da azabtarwa - wanda ya shahara da haifar da yawaitar gudun hijira da kuma gwagwarmayar yau da kullun don shawo kan hatsarin da za a iya fuskanta, inda kuma fararen hula ke ci gaba da ke rayuwa a cikin yanayi da ya bayyana a matsayin wanda ba za a iya jurewa ba.

A farkon rikicin, ya shaida kisan wani farar hula a lokacin binciken ababen hawa na yau da kullun a Khartoum.

Ya ce, "Ya yi kokarin bayyana kansa," "kuma suka harbe shi har lahira a gabanmu." Labarinsa yana daya daga cikin irin wadannan abubuwan da ma’aikatan lafiya ke bayarwa a karkashin yankunan da RSF ke iko da su.

A cewar Dr Muhammad, mayakan RSF sun yi masa barazana kai tsaye, suna sukar goyon bayan da yake nunawa ga SAF da kuma matsa masa lamba kan ya koma aiki da su. Lokacin da ya ƙi, sai suka ƙara tsananta barazanarsu gare shi.

Yana bayar da rahoton yadda ake cin zarafin likitoci a wuraren bincike, ana garkuwa da su, ana kai musu hari, ko kuma ana tilasta musu yin tiyata ga manyan mambobin RSF.

Tunda Muhammad ya bayyana cewa ma'aikatan lafiya sun fuskanci "sace su zuwa yankunan da ba a sani ba" kuma neman ‘yan uwansu da su biya kudin fansa. Ya kuma ce an "tilasta wa ma'aikatan lafiya yin abin kunya na aika saƙonni cewa lamarin yana da kwantar da hankali kuma rayuwa na tafiya kalau babu wata matsala."

A cewar Muhammad, halin da ake ciki a Al Fasher a lokacin mamayar RSF ya kasance mummunan bala'i. Ya ce yayin da sojojin RSF suka faɗaɗa ikonsu a cikin birnin, "kisan kiyashi, kawar da wata kabila, cin zarafin mata, da kashe marasa lafiya a cikin asibitoci" ya faru.

Kukan da ƙasashen duniya suka yi ya haɗa da kiran gaggawa na a sanya RSF a matsayin ƙungiyar ta'addanci. Sojojin Sudan sun mayar da martani ta hanyar sanar da shirin yaƙi gaba ɗaya da kuma bayyana cewa za su hana RSF ci gaba zuwa sauran yankunan arewa.

Dakta Tijani ya kiyasta cewa adadin wadanda suka mutu a yankin Al Fasher ya kai dubunnan daruruwan - adadi da ba za a iya tantancewa ba, amma kuma yana nuna girman tsoro da barnar da wadanda suka tsira suka shaida.

Rashin kayan kula da lafiya

Muhammad ya bayyana yanayin jinkai ga al'ummomin da suka rasa gidajensu a matsayin mai matuƙar tsanani. Ya ce fararen hula da ke tsere wa daga Al Fasher zuwa Tawila, Karnoy, Ambro da Al-Dabba an "kai musu hari, an yi musu duka kuma an ci zarafinsu" a kan hanya, wasu kuma sun mutu sakamakon "harbin bindiga, yunwa, ƙishirwa ko gajiya."

Ya ƙara da cewa wani ɓangare ne kawai ya sami damar isa yankunan da sojoji ke da iko da su, inda cibiyoyi da al'ummomi ke ba da mafaka na ɗan lokaci, abinci da taimakon likita marar yawa.

Khartoum na fuskantar wata matsala daban amma ita ma mai kawo cikas. Hanyoyin ruwa sun lalace, katsewar wutar lantarki ta ci gaba da ƙaruwa, kuma tarin shara ya haifar da yanayi da Muhammad ya ce ya dace da yaɗuwar cututtukan da ake ɗauka ta hanyar shakar isaka da kuma waɗanda ake ɗauka ta hanyar amfani da ruwa.

A cewar UNICEF, an sami rahoton kamuwa da cutar kwalara sama da 7,700 da mace-mace 185 a Jihar Khartoum tun farkon 2025 - ciki har da kamuwa da cututtuka tsakanin yara 'yan ƙasa da shekara biyar sama da 1,000 - yayin da cutar ta yaɗu cikin sauri a unguwannin da ba su da tsarin ruwa mai tsafta da tsaftar muhalli.

Kamuwa da cutar zazzabin dengue ma ta ƙaru. Kungiyoyin kare hakkin dan adam da ke rawaito bayanai daga Ma'aikatar Lafiya ta Tarayya sun bayar da rahoton sama da mutane 14,000 da suka kamu da cutar dengue a Jihar Khartoum tun daga watan Janairun 2025.

Rushewar tsarin kula da lafiya ma ya yi tsanani. Fiye da kashi 60 cikin 100 na asibitoci a babban birnin Khartoum an rufe su, an yi musu fashi ko kuma suna aiki ba tare da isasshen ƙarfin da za su iya aikin ba, a cewar kungiyar Kare Hakkokin Yara ta ‘Save the Children’.

A yayinda ake tsaka da fuskantar wannan rugujewar, matasan 'yan jarida da fararen hula na Sudan suna tattara bayanai da kuma daidaita kansu a sabon yanayin da suka shiga.

Dan jarida Awad, wanda ya ce dole ne ya katse karatunsa na aikin jarida saboda yakin, ya kammala su ta yanar gizo yayin da fada ke kara ta'azzara. Ya kamu da zazzabin dengue amma tun daga lokacin ya warke, yana mai lura da cewa kamuwa da cutar "na damun mutane sosai."

Ya bayyana yadda abokan aikinsa da yawa suka tsere daga kasar kuma suka ci gaba da zama ba aikin yi. "Ina kewar zama a Khartoum sosai," in ji shi, yana nuna sha'awar rayuwar jama'a ta yau da kullun maimakon kwanciyar hankali da ya samo asali bayan rikici.

Don fahimtar abubuwan da ke haifar da wannan rugujewar, dan jarida Awad ya kara komawa ga manufar Yakin Zamani na Hudu (4GW). Tsarin yakin ya bayyana rikice-rikice da a cikin su ake lalata kayan gwamnati da raunana su ba wai kawai ta hanyar fadan soja kai tsaye ba, har ma ta hanyar wargaza zaman lafiya - ta hanyar rashin bayanai, matsin lamba na tunani, lalata tattalin arziki, dabarun sauya tunani da kuma ingiza wakilan kare manufofi a cikin gida.

A ra'ayin Awad, kungiyoyi masu dauke da makamai na kasashen waje a Sudan sun yi amfani da rarrabuwar kawuna da siyasa da ke akwai, suna hanzarta rushewar hukumomin gwamnati da kuma lalata amincewar jama'a ga mahukunta.

Ya yi jayayya cewa ikon da RSF ke da shi kan ma'adinan zinare, hanyoyin kasuwanci da hanyoyin fasa-kauri - tare da zargin cewa suna samun goyon baya daga waje - ya bai wa 'yan bindigar damar yin aiki a matsayin kishiyar gwamnati a lokaci guda, wanda hakan ke kawo cikas ga ikon mallakar kasa.

Samar da hanyoyin kai kayan jinkai

Likita a Sudan kuma shugaban kungiyar likitocin Sudan, Dr. Yasser Ahmed Ibrahim ya bayyana cewa rikicin da ake yi a yanzu yana maimaita abubuwan da ba a warware su ba na tarihin Sudan, musamman tun zamanin Mahdiyya (1881-98).

Dr. Ibrahim ya shaida wa TRT World cewa rashin yin nazari sosai kan wadannan al’amuran na tarihin ya ba da damar sake bullowar irin wannan yanayi na tashin hankali.

Mutanen da aka yi hira da su sun bayyana tasirin yakin a kan al'ummar Sudan a matsayin babba. Dr. Tijani, wanda ya kula da iyalan da aka raba da matsugunansu ko suka tsere daga tashin hankali, da kuma dan jarida Muhammed Nazar Awad sun bayyana irin wannan mummunan hali a matsayin abin da ya fi komai muni.

Yara sun fuskanci mummunan zalunci; mata sun ba da rahoton cin zarafi a yankunan da ake rikici; an raba iyalai da juna; hanyoyin rayuwa sun ruguje; kuma suna gargadin cewa radadin bayan rikici na zama mai tsalakawa daga zamani zuwa wani zamanin.

Kusan rushewar ayyukan kula da lafiyar kwakwalwa gaba daya ya bar miliyoyin mutane ba tare da taimako ba.

Duk da wannan tabarbarewa, shaidun da aka samu a fagen sun nuna cewa fararen hular Sudan, likitoci, 'yan jarida da cibiyoyin cikin gida na ci gaba da tabbatar da dorewar juriyar al'umma. Cibiyoyin sadarwa na yau da kullun suna ba da abinci, matsuguni da magunguna lokacin da hanyoyin gwamnati suka gaza.

Likitoci da ma'aikatan agaji sun ce haɗin kan al'umma ya kawar da samun asarar rayuka da yawa a wasu yankunan.

Duk da haka, Awad ya yi gargaɗin cewa wannan juriya ba ta da iyaka. A ra'ayinsa, ba tare da samun kari mai yawa a cikin ayyukan ƙasashen duniya ba - musamman wajen tabbatar da hanyoyin jinkai, kare ma'aikatan lafiya da dawo da muhimman ayyuka - sakamakon na iya zama wanda ba za a iya gyarawa ba.

Rikicin Sudan ba abinda za a yi hasashensa ba ne; yana faruwa a ainihin lokaci. Masu sharhi sun ce rugujewar tsarin lafiyarta alama ce da ke bayyana gazawar gwamnati.

Kamar yadda Dr Tijani ya yi gargaɗi, yanzu al'ummar duniya na fuskantar yanke wani mataki mai hatsari da muhimmanci: shiga tsakani ta hanya mai ma'ana don hana ci gaba da tabarbarewa, ko kuma fuskantar hatsarin ganin wargajewar ƙasar da mutanenta suka riga suka jure wa halin da ba a iya jure masa.