Ra'ayi
SIYASA
5 minti karatu
Daga Baghdad zuwa Abuja: Tsohon tuggun Amurka da sunan ‘yanci da mamaya
Ikirarin Trump na ana aikata kisan kiyashi ga Kiristoci a Nijeriya da barazanar kai hari kasar sun zama maimaicin kwadayin mamaya da sunan nuna damuwar jinkai.
Daga Baghdad zuwa Abuja: Tsohon tuggun Amurka da sunan ‘yanci da mamaya
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar daukar matakin soji a Nijeriya saboda cewar wai ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Nijeriya.
6 awanni baya

Daga Abu Bilaal Abdulrazaq bn Bello bn Oare

"Macijin da ke yi maka fito na duba ta yadda zai matso kusa ya sare ka ne kawai."

Wannan tsohon karin magana ne na Afirka da ke gargaɗi game da ruɗani - domin idan mutane suka yi sha'awar yarda da kowane irin labari na ƙasashen waje, suna fuskantar hatsarin rasa fahimtar hukunci da ikon mulkinsu.

Wannan, abin baƙin ciki ne, kuma ita ce hanyar da Nijeriya ke bi bayan sanarwar shugaban Amurka Donald Trump, inda ya sake fasalta Nijeriya a matsayin Ƙasa Mai Damuwa ta Musamman kuma yana zargi ba tare da wata hujja mai inganci ba, cewa Kiristoci a Nijeriya sun kasance waɗanda ake yi wa kisan kare dangi.

Zargin Trump marar tushe, wanda aka ɗora a doron maganganu na baki kawai kuma goyon bayan barazanar shiga tsakani, na iya ƙara rura wutar wata ƙasa da ta riga ta yi rauni.

Ya yi gargaɗin cewa idan gwamnatin Nijeriya "ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da duk wani taimako ga Nijeriya nan take, kuma za ta iya shiga cikin wannan ƙasar da yanzu ta zama abin kunya don kawar da 'yan ta'adda Musulmai waɗanda ke aikata waɗannan munanan ayyukan na ta'addanci gaba ɗaya".

Kalamansa na barazanar ƙara rashin yarda tsakanin al'ummomin da suka shafe shekaru suna fama da rashin lafiya daga raunukan kabilanci da na addini.

Daga Iraki zuwa Libya, daga Afghanistan zuwa Somalia, mamayar Amurka ta bar ƙasashe cikin rugujewa - sun wargaje, sun kacalcale, kuma sun fi yin muni fiye da yadda suke a baya kafin ta mamaye su.

Suna ambatar dimokuradiyya, ‘yanci ko damuwar jinkai a matsayin halascin mamayar kasashen. Amma idan kurar ta lafa, sai a fahimci ‘yantarwa da ake magana ta haifar da rikice-rikice, rasa rayuka da shekaru na rashin zaman lafiya.

Yin tunanin cewa Najeriya za ta iya zama daban a ƙarƙashin irin wannan "damuwa" na nufin yin watsi da amo mai karfi na tarihi.

Kawar da gaskiya don biyan bukatar kai

Kalamin Trump game da "kisan kare dangi ga Kiristoci" a Nijeriya babban kuskure ne.

Bayanan gaskiya da ake da su sun nuna cewa tashin hankali a Nijeriya - ko ma daga Boko Haram, 'yan fashi, rikicin makiyaya da manoma ko rikicin ƙabilanci - ya jawo asarar rayukan Musulmai da yawa, galibi fiye da Kiristoci.

An taba kashe dukkan al'ummar Musulmi a yankin Arewa Maso Gabas.

An lalata masallatai. An kashe malaman Musulunci. Manoma a yankunan da galibinsu Musulmi ne ba sa iya zuwa gonakinsu tsawon shekaru.

Sojojin Nijeriya sun kafa wuraren binciken ababan hawa marasa adadi, kuma dukkan garuruwa sun koma kufai. Duk da haka babu wani - aƙalla manyan ƙasashen Yamma - da ya taɓa kiran lamarin kisan kare dangi ga Musulmai.

Yunkurin sanya rikicin tsaro mai sarkakiya a Nijeriya a matsayin kawar da mabiya wani addini ba komai ba ne illa zabin fahimta da kuma manuba a kafofin watsa labarai.

Mafi muni ma, batun na da hatsarin mayar da 'yan Nijeriya suna yakar juna, mabiya addinai daban-daban na hantarar juna, ‘yan kasa su yaki ‘yan kasa, a lokacin da aka fi bukatar hadin kan juna.

Munafurcin ya fi muni idan aka kalli abubuwan da ke faruwa a wajen Nijeriya.

Ya zuwa ranar 3 ga Nuwamban 2025, an kashe mutane sama da 68,858 kuma sama da 170,664 sun jikkata a Gaza, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu da ke Gaza, daga cikin al'umma kusan miliyan 2.2.

Duk da haka Trump bai ayyana Gaza a matsayin "ƙasar da ke da matukar damuwa ba".

Bai yi kira da a shiga tsakani a can ba. Me ya sa? Domin wadanda abin ya shafa galibi Musulmai ne. Munafurcin a bayyane yake karara, kuma rashin daidaiton ɗabi'a yana damun mutane.

Idan gaskiya ne, Amurka ce da kanta ta daɗe tana yaƙi da ƙasashen da suka fi rinjayen Musulmi a ƙarƙashin wasu siffofi daban-daban - yaƙi da ta'addanci, zaman lafiya, da kuma ceto jama'a.

Bai kamata Nijeriya ta zama filin yin irin wannan mummunan wasa na gaba ba.

Ba za mu iya barin labaran wata babbar kasa su bayyana ko su wanene mu ba, menene ma'anar rikice-rikicenmu, ko kuma yadda ya kamata a mulki kanmu.

Nijeriya ƙasa ce mai 'yancin cin gashin kai. Gwamnatinta ta sha musanta duk wani ikirarin kisan kare dangi ga Kiristoci.

Babu wani shugaban ƙasa na waje, komai ƙarfinsa ko muryarsa, da ke da 'yanci ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa na ƙaddamar da ayyukan soji a cikin iyakokin ƙasarmu.

Yin hakan zai zama aikin zalunci, a bayyane karara.

A waɗannan lokutan, ya zama dole 'yan Nijeriya su yi tunani mai zurfi. Babban hatsarin ba wai kawai maganganun Trump ba ne - ya rage namu da mu yarda da hakan.

Kamar yadda masu hikima ke faɗi, "Lokacin da wani ya gaya maka miyar mahaifiyarka ta fi taka daɗi, yana miƙa hannunsa ne kawai don ya ɗauki cokalinka."