Ministan Kuɗin Ghana Dakta Cassiel Ato Forson ya gabatar da kasafin kuɗin gwamnatin ƙasar na shekarar 2026 ga majalisar dokoki a madadin Shugaba John Dramani Mahama.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar Ghana ya ambato ministan yana cewa “adadin kuɗin da [gwamnatin] za ta kashe zai kasance GHc biliyan 302.5.”
Kuɗin zai kai kimanin naira tiriliyan 40 idan aka sauya shi zuwa naira daga kuɗin Ghana.
Dakta Forson ya ce kasafin kudin ya nuna wani babban sauyi daga “farfaɗowa zuwa canji, da kuma juriya zuwa himmar aiki da kuma ɗorewar ayyukan yi,” yana mai bayyana matakan ƙarfafa ɗorewar tattalin arziki da hanzarta samar da ayyukan yi da kuma ƙarfafa fannonin zamantakewa.
“An yi ƙiyasin cewa albashin ma’aikata zai kai GHc biliyan 90.3 (kimanin naira triliyan 12), domin tabbatar da biya da ya dace ga ma’ikatan gwamnati,” in ji ministan kuɗin.
Ya bayyana cewa gwamnatin ta sake dawo da tsarin tsimi a fannin kuɗi da daidaita kuɗin cedi da rage hauhawar farashi da kuma sake ƙara ƙarfafa ƙwarin gwiwar masu zuba jari.
Kazalika ya ce kuɗaɗen da gwamnatin Ghana ke son kashewa kan ababen more rayuwa GHc biliyan 57.5 (kimanin naira tiriliyan 7.4 idan aka sauya kuɗin zauwa naira).
Ministan ya ce kasafin kuɗin shekarar 2026 ya mayar da hankali ne kan abubuwa uku masu muhimmanci — tsimi mai ɗorewa a harkar kuɗi da kula da bashi yadda ya dace da kuma zuba jari a kan ababen more rayuwa da harkar noma domin samar da ayyukan yi da kuma inganta ilimi da lafiya da tsaro da ci-gaba na bai ɗaya.
A shekarar 2026 dai gwamnatin ƙasar tana sa ran samun kuɗi da ya kai GHc biliyan 286.1( kimanin naira tiriliyan 37) ta hanyar haraji.

















