Mitumba: Sake tunani game da kasuwancin tufafin gwanjo a Afirka
AFIRKA
8 minti karatu
Mitumba: Sake tunani game da kasuwancin tufafin gwanjo a AfirkaAn gaza amsa babbar tambayar: Shin kayan gwanjo da ke karuwa a kasuwanni na da muhimmanci ga rayuwar miliyoyin mutane ko kuma wani sabon nau’in mulkin mallaka ne a boye?
Kasashen Afirka na gogaro da kayan gwanjo da ake shigar da su daga kasashen yammacin duniya da Larabawan Gabas ta Tsakiya. / AFP
12 Janairu 2026

Saboda yawan amfani da tufafi da ake yi, ana jigilar kayan sawa na hannu da ake kira gwanjo zuwa tashoshin jiragen ruwa na Afirka, galibi a ƙarƙashin sunan "sadaka." A ƙarshe, kwandon sharar kayan Yammacin duniya ya zama matsalar wanzuwar Afirka.

Abin da aka tsara a matsayin karamci, a aikace, wani kasuwanci ne na miliyoyin daloli, tare da ƙungiyoyin agaji da kamfanonin sake sarrafa kayayyaki ke sayar da waɗannan gudunmawar don samun riba.

Ba kamar musayar hajoji a kasuwa ta yau da kullum ba, tsarin na aiki matsayin sharar zubar da tattalin arziki, tare da sayar da tufafi akan farashin da ke dakile masana'antun gida, kuma yana hana masana'antar cikin gida bunkasa yayinda take ƙara dogaro da kayan da aka zubar da su na ƙasashen yamma.

Shekaru da yawa, ƙasashen Afirka sun shiga cikin wata dangantaka mai rikitarwa, suna kai komo tsakanin yunƙurin hana cinikin gaba daya da nuna rashin amincewa.

An gaza amsa babbar tambayar: Shin kayan gwanjo da ke karuwa a kasuwanni na da muhimmanci ga rayuwar miliyoyin mutane ko kuma wani sabon nau’in mulkin mallaka ne a boye?

Afirka mai samar da kayan amfani da ake sarrafawa ta zama mai sanya tufafi gwanjjo.

Duk da cewa ƙasashen Afirka da yawa suna cikin manyan masu samar da kayan samar da tufafi a duniya, nahiyar ta yi baya sosai a fannin masana'antar kera tufafin.

Waɗannan ƙasashe masu noman auduga suna ƙarewa da sayen kayayyakin da aka gama amfani da su a kasashen Yamma, kuma ba su da wata sauran daraja. Ga yawancin 'yan ƙasashensu matalauta, tufafin da aka yi amfani da su waro gwanjo ne kawai zaɓin da ya dace.

An san su da sunan "mitumba" a Gabashin Afirka, "okrika" a kudancin Nijeriya, Gwanjo a arewacin Nijeriya da "salaula" a Zambia, mutanen kasashen Yamma ne suka bayar da kyautar waɗannan tufafin, amma sai manyan ƙungiyoyin agaji da kamfanonin sake amfani da su na kasuwanci suka tattara, suka tace su, sannan suka sayar kafin su isa kasuwannin Afirka.

Ba wai kawai hanyar yin sayayya mai araha ba ce, sun zama hanyar dogaro da kai ga miliyoyin mutane. Masu sayarwa suna siyan kayan kuma suna sayar da kowannen kayan daban-daban a kasuwannin da ke cike da jama'a, suna samun abin rayuwa a wurare mafi wahalar sha’ani.

Amurka ta yi barazana, kasuwancin na cikin hatsari

Tashin hankali tsakanin haramta cinikin da kuma kare kayayyakin more rayuwa ya kai wani sabon matsayi a shekarar 2016.

Kungiyar Kasashen Gabashin Afirka (EAC) ta amince da hana shigo da kayan da aka yi amfani da su ya zuwa shekarar 2019, matakin da zai kai ga wadatar da kansu d akansu da kayan sawa.

Wannan buri ya lalace cikin sauri lokacin da gwamnatin Trump ta yi barazanar korar ƙasashen daga Dokar Ci Gaban Afirka da Dama (AGOA), babbar yarjejeniyar cinikayya ta Amurka wadda ke ba da damar samun shiga kasuwa mafi kyawu.

Duk da cewa tanade-tanaden AGOA sun daɗe suna tsara yanayin ciniki, izininta ya ƙare a watan Satumban 2025 a tsakanin rashin tabbas na yiwuwar sabuntawa, hakan na sake nuna yadda ƙarfin tattalin arzikin ƙasashen yamma ya ci gaba da fifita damar shiga kasuwa fiye da haɗin gwiwar masana'antu.

Wannan matakin ya fito da ainihin gaskiyar dangantakar: Yammacin duniya zai fi son Afirka ta ci gaba da zama kasuwa ga tufafinta da aka watsar maimakon zama mai fafatawa da masana'antu.

A ƙarƙashin matsin lamba mai yawa, EAC ta soke haramcin. Dalilan sun wuce na siyasa yanzu inda suka zama na gaskiyar rayuwar yau da kullunm.

Cinikin tattalin arziki ne mai faɗi, wanda ba na yau da kullum ba. A Kenya kaɗai, yana samar da ayyukan yi ga mutane kusan miliyan biyu.

Ga al'ummomin da ke da ƙarancin kuɗi, mitumba na ba da fa'idoji bayyanannu na farashi, inganci da nau'ikan da masana'antar gida ba za ta iya samar da su ba.

Tambayar da Abdullah, wani mai sayar da kayayyaki na tsawon lokaci a Tanzania ya yi, ta nuna irin wannan mummunan yanayi: "Wa zai iya sayen sabbin tufafi?" Zaɓi ne tsakanin sanya tufafin da aka yi watsi da su na Yammacin duniya ko kuma yawo babu sutura.

Wannan fifiko ba wai kawai tattalin arziki ba ne. Riga gwanjo da aka kawo daga Turai ko Amurka galibi na ɗauke da wani sako mai ƙarfi na al'adu, alama ta inganci da zamani wanda a wasu lokutan sabbin tufafi da ake samar da su a cikin gida ba su da su.

Wannan yana haifar da mummunar alaƙar tunani: dogaro da kayan da Yammacin duniya ke yi yana ƙarfafa su ta hanyar yarda da ke cikin gida game da fifikonsu.

Mitumba a matsayin matain farko na kwashe arziki

Wannan danwaken zagaye na tattalin arziki da ake dogaro a kai na buɗe ƙofar zuwa wani rikici mafi rikitarwa. Ba duk kayan da aka yi amfani da su daga Yammacin duniya za a iya sanaya wa ba.

Bincike daga Gidauniyar OR da ke Ghana ya nuna cewa ingancin tufafi gwanji na raguwa kowace shekara, inda wani ɓangare na yawan jama'a ba za a iya sayar da shi ba kuma yana haifar da matsalar sharar gida ga ƙasashen da ke karɓar kayayyaki.

Wannan ya mayar da yanayin ƙasa a ƙasashe kamar Ghana zuwa makabartar tuddan yadudduka, inda yadi na roba da ba sa narkewa ke zubar da guba cikin ƙasa da ruwa, kyauta ta ƙarshe, mai guba daga kayan gwanjo.

Wannan yana hanzarta ɗumamar yanayi kuma yana ƙara lalata muhalli

An akwai rashin daidaito sosai: Arewacin Duniya na samun riba daga yawan samar da kayayyaki da shararsu, yayin da ƙasashen Afirka ke shan wahalarsu.

A ƙarƙashin "bayar da gudunmawa," Arewacin Duniya na zubar da gubar kayan da ta gama amfai da su a Afirka, tana kiyaye nata gidan mai tsafta.

Wani mawuyacin hali na Afirka shi ne cewa kasuwar mitumba, a matsayin "kasuwar bayan fage ta tattalin arziki," ta kawar da masana'antun gida gaba ɗaya.

A yau, miliyoyin mutane sun dogara da wannan fanni na kayan gwanjo don abincinsu na yau da kullum, amma babu wani tsarin samar da kayayyaki na cikin gida mai dorewa.

Masana'antun cikin gida a nahiyar har yanzu suna ganin yana da wahala a iya kallon kayan aikinsu a matsayin manyan masana'antun samar da tufafi ko ma a yi gasa da su da na kasashen waje.Kayan da ake kawo wa daga waje ba wai suna ba wa jama’a kudi ba ne, hanya ce ta dogaro a kan wani.

Idan wata rana Yammacin duniya suka yanke shawarar yanke waɗannan "abin da ake kira tallafin kuɗi," za a bar Afirka ba tare da masnaa’antun samar da tufafi ba, ba tare da hanyoyin da za ta ba wa matasa ayyukan yi ba.

A wata ma'anar, nahiyar da ta dogara da sharar ƙasashen yamma za ta kasance tsirara a fannin tattalin arziki da zamantakewa idan wannan bayar da taimakon ya tsaya.

Samar da sabuwar makoma

Saboda haka, shugabannin Afirka za su iya karya wannan tsarin. Manufar ba za ta zama haramci kawai ba tare da wata hanya mai ƙarfi ba da za ta maye gurbinsa, dole a samar da tsari mai kyau da zai farfado da masana’antun cikin gida.

Wannan na nufin sake buɗe masana'antu da aka rufe, ƙarfafa wa matasa 'yan kasuwa, da kuma dawo da al'adun saƙa na nahiyar masu tushe, masu inganci, ba wai kawai a matsayin gadon ado ba, har ma a matsayin tushen 'yancin kai a fannin tattalin arziki.

Yau nahiyar ta riga ta fara hulda da masu samar da tufafi daga China da Kudancin Asiya zuwa Gabas ta Tsakiya, kowanne na gabatar da farashi mabambanci, da kuma kasuwancin dogaro kan wasu.

A cikin wannan yanayi, wasu daga masu fitar da kayayyaki ke nuni ga kasashe irin su Turkiyya, tare da wasu, wadanda kayayyakinsu suka fi karfi da inganci, na iya zama abokan hula na wani dan lokaci ba wai sauyi na dindindin ba.

Mu’amala da irin wadannan kawaye don musayar dabaru da hikimomi, ko daidaita kasuwanci na iya taimaka wa manufofin nahiyar na zaman kanta da samar da nata masana’antun.

Karfin Afirka ya dogara ne ba a kan kayan da ake sayo wa daga Yammacin duniya ba, a’a ya dogara ne kan yadda ta sake fasalta makomarta. Makoma ba mai amgani da tarkacen wasu kasashen ba, a’a mai samar da nata kayan da kanta ta hanyar habaka masana’antu.

Marubuciyar, Sare Şanlı, mai sharhi ce wadda ta ƙware a siyasar Afirka da dangantakar karfin ikon duniya a nahiyar.

Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba lallai ne su yi daida da ra’ayin dab’i na TRT Afrika ba.