NIJERIYA
5 minti karatu
Gwamnatin Nijeriya ta kai ƙarar Sowore da Meta da X kotu kan cin fuskar Tinubu
Lauyoyin Sowore sun ƙara da cewa dole Meta da X su gane cewa a muddin suka yi biyayya ga buƙatar gwamnatin Nijeriya ta hana tofa albarcin baki, to sun saɓa wa doka kuma sun zama masu hannu a laifin danne gwagwarmayar samun ‘yanci.
Gwamnatin Nijeriya ta kai ƙarar Sowore da Meta da X kotu kan cin fuskar Tinubu
Mai fafatuka Omoyele Sowore ya ce ba zai goge saƙon da ya wallafa ba / Reuters
4 awanni baya

Hukumar tsaro ta farin kaya ta Nijeriya (DSS) ta shigar da ƙara a kotun tarayya da ke Abuja inda ta zargi fitaccen ɗan gwagwarmayar nan Omoyele Sowore da wallafa saƙo a shafukan sada zumunta na cin fuska ga shugaban ƙasar Bola Tinubu.

Hukumar ta bayyana kamfanonin sada zumuntan X  da Meta Inc. a matsayin waɗanda ake tuhuma tare da shi.

Wani darakta na gabatar da ƙara a ma’aikatar shari’a, Muhammed Abubakar, tare da wasu lauyoyin DSS, sun shigar da ƙara a madadin hukumar da gwamnatin Nijeriya.

A saƙon da ya wallafa a shafinsa na X ranar 25 ga watan Agusta, Mista Sowore ya soki ziyarar da shugaban Nijeriya ya kai Brazil da kuma kalaman da shugaban ya yi yayin ziyarar.

“Mai laifi @officialABAT (Bola Tinubu) ya je Brazil inda ya ce babu cin hanci da rashawa a Nijeriya a gwamnatinsa. Ji wani ƙarfin hali na ƙarya ba tare da kunya ba!”— in ji Omoyele Sowore.

Sai dai a ranar 8 ga watan Satumba DSS ta bai wa Sowore wa’adin mako ɗaya ya cire abin da ta kira saƙon “ƙarya da da cin fuska da kuma tunzura jama’a game da Shugaba Bola Tinubu.”

Ranar Litinin ne wa’adin ya ƙare ba tare da Sowore ya cire saƙon da ya wallafa game da Shugaba Tinubu ba.

Kazalika, kamfanonin sada zumunta, X Corp da Meta Incorporation mamallakin X da Facebook, ba su bi umarnin DSS na neman cire saƙon Sowore ba.

Ƙarar Sowore

Shi ma Omoyele Sowore ya shigar da ƙararraki biyu na kare ‘yancin ɗan’adam a babbar kotun tarayya da ke Abuja kan DSS da kamfanonin sada zumunta na Meta da X.

Wata sanarwar da lauyoyinsa suka fitar ranar Talata kuma Tope Temokun ya sanya wa hannu domin ƙalubalantar abin da lauyoyin suka kira ‘hana tofa albarkacin baki da ya saɓa wa tsarin mulki’ kan shafukan Sowore a kafofin sada zumunta na Meta da X.

Temokun ya ce ƙarar ta bayyana kai-tsaye cewa wannan batu ne na ɗorewar ‘yancin tofa albarkacin baki a Nijeriya, yana mai ƙarawa da cewa “idan hukumomin gwamnati za su iya umurtar manyan kafofin sada zumunta na duniya game da wanda zai iya magana da abin zai iya faɗa, babu wani ɗan Nijeriya da ya tsira, za a rufe bakunansu bisa umarnin waɗanda ke kan mulki.”

“Hana suka na siyasa abu ne da ba shi da gurbi a dimokuraɗiyya. Kundin tsarin mulkin Nijeriya, sashe na 39, ya tabbatar wa ko wane ɗan ƙasa ‘yancin tofa albarkacin baki ba tare da  tsangwama ba. Babu wata hukumar tsaro, duk ƙarfinta da za ta iya dakatar da ko kuma kawar da wannan ‘yancin.”

Lauyoyin Sowore sun ƙara da cewa dole Meta da X su gane cewa a muddin suka yi biyayya ga buƙatar gwamnatin Nijeriya ta hana tofa albarcin baki, to sun saɓa wa doka kuma sun zama masu hannu a laifin danne gwagwarmayar samun ‘yanci.

Kalaman Tinubu a Brazil

A lokacin da ya kai ziyara ƙasar Brazil dai, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa sauye-sauyen da gwamnatinsa ta yi a Nijeriya sun kawo ƙarshen cin hanci a ƙasar.

“Sauyen-sauyen da na ƙaddamar tun da na karɓi ragamar mulki a Nijeriya suna tasiri sosai. Zan iya bugun ƙirji kan haka. Daga farko sun ba da wahala. Amma a yau sakamakonsu yana haɓaka,” in ji Shugaba Tinubu.

 “Yana daɗa bayyana ga mutane. Mun ƙara yawan kuɗi cikin tattalin arzikinmu. Yanzu babu cin hanci da rashawa. Gwamnan babban bankin [Nijeriya] ya zo nan. Ba sai ka san shi ba kafin ka samu takardun kudin ƙasashen waje da kake buƙata,” in ji shi.

“An kawar da ‘yan bunburutu daga kasuwar musayar kuɗaɗenmu. Ƙofa a buɗe take ga cinikayya shiga cikin sauƙi, fita cikin sauƙi,” a cewarsa.

Martanin Sowore

Shi kuwa ɗan fafatuka, Omoyele Sowore, wanda hukumar DSS take ƙorafi game da saƙon da ya wallafa ya mayar da martani da saƙon DSS.

“Da safiyar yau, X (wadda ake ce wa Twitter a da) ta tuntuɓe ni a hukumance game da wasiƙar barazana da suka samu daga hukumar DSS mara bin doka game da saƙon da na wallafa kan Tinubu. Ba zan goge saƙon ba,” in ji Sowore.

Gwamnatin Nijeriya ta taɓa haramta amfani da shafin X

Wannan dai ba shi ne karon farko da aka fara samun sa-in-sa tsakanin gwamnatin Nijeriya da kafar sada zumuntar X ba.

Ko a tsakanin shekarar 2021 zuwa shekarar 2022 ma sai da ƙasar ta haramta amfani da shafin na X na watanni bakwai bayan shafin ya goge wani saƙo da shugaban ƙasar Nijeriya na lokacin, marigayi Muhammadu Buhari, ya wallafa a shafinsa na X.

A saƙon nasa da X ya goge Buhari ya ce waɗanda suke neman kafa ƙasar Biafra ba su san irin abin da aka yi ba a lokacin yaƙin basasar Nijeriya kuma gwamnati za ta bi da su ta hanyar da suka fi ganewa.

Bayan goge wannan saƙon ne gwamnatin Nijeriya ta hana amfani da shafin na X a ƙasar, har sai lokacin da shafin ya cika wasu ƙa’idojin da gwamnatin ta gindaya masa.