Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ta ragu a karo na biyar a jere a watan Agustan shekarar 2025, lamarin da zai kawo sassauci ga mutanen da ke fama da tsadar rayuwa, in ji hukumomin ƙasar.
Alƙaluman da Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya ta fitar ranar Litinin sun nuna cewa hauhawar farashin ta ragu zuwa kashi 20.12 cikin 100 daga kashi 21.88 cikin 100 da ta kasance a watan Yuli.
Alƙaluman sun nuna raguwa na kashi 1.76 cikin 100 daga wata zuwa wata, abin da ke nuna gagarumar raguwa daga kashi 32.15 cikin 100 da aka samu a watan Agustan shekarar 2024.
Alƙaluman, da ke bibiyar yadda matsakaicin farashin kayayyakin yau da kullum ke sauyawa, sun bayya cewa farashin kayayyaki sun ƙaru da maki 126.8 a watan Agusta daga maki 125.9 a watan Yuli.
An samu sassaucin hauhawar farashin kayayyaki a Afrilu a Nijeriya – NBS
Hauhawar farashi ta wata-wata ta tsaya a kashi 0.74 cikin 100, ƙasa da kashi 1.99 cikin 100 na watan Yuli, lamarin da ke ishara ga raguwar hauhawar farashi a faɗin ƙasar.
Rahoton ya bayyana cewa, “Gwajin farashin kayayykin da ake saya ya ƙaru zuwa maki 126.8 a watan Agustan shekarar 2025, lamarin da ya nuna ƙari na maki 0.9 daga watan da ya gabata (125.9).
“A watan Agustan shekarar 2025, hauharar farashi ta ƙaru zuwa kashi 20.12 cikin 100 idan aka kwatanta da watan Yuli na shekarar 2025 inda hauhawar farashi ta kai kashi 21.88 cikin 100,” in ji NBS.
“Idan aka yi la’akari da sauyin, hauhawar farashin watan Agustan shekarar 2025 ta ragu da kashi 1.76 cikin 100 idan aka yi kwatanta da ta watan Yuli na shekarar 2025.”
Hukumar ta bayyana cewa akwai rashin daidaituwa a matsin hauhawan farashin a birni da ƙauye. Hauhawar farashi a birni ta ragu zuwa kashi 19.75 cikin 100 a watan Agusta daga kashi 34.58 cikin 100 da yake a shekarar da ta gabata, yayin da hauhawar farashi a karkara ta ɗan fi shi inda take kashi 20.28 ci,kin 100 idan aka kwatanta da kashi 29.95 cikin 100 da yake a watan Agustan shekarar 2024.
Idan aka dubi wata zuwa wata kuwa, hauhawar farashi a birane ta ragu zuwa kashi 0.49 cikin 100 daga 1.86 cikin 100 na watan Yuli, yayin da hauhawar farashi a karkara take kashi 1.38 cikin 100 daga kashi 2.30 cikin 100.