Yadda ƙasaitaccen bikin 'yar hamshakin attajirin Nijeriya Femi Otedola, Temi ya ɗau hankali
Yadda ƙasaitaccen bikin 'yar hamshakin attajirin Nijeriya Femi Otedola, Temi ya ɗau hankali
An ɗaura auren masoyan ne a wani Coci da ke babban birnin Iceland a ranar 8 ga Agustan 2025, amma sai a kwanan nan aka fitar da bidiyon shagalin bikin.
9 Satumba 2025

Ƙasaitaccen bikin ‘yar hamshakin attajirin Nijeriya Temi Otedola da fitaccen mawaƙi Mr Eazi ya samu halartar hamshakin attajirin Afrika a wurin da ke nesa da Nijeriya da kilomita 7,000.

Temi mai shekaru 29, ‘ƴa ce ga hamshakin ɗan kasuwar Nijeriya Femi Otedola, wanda ke cikin attajirai 20 na Afirka a yanzu.

Angon Temi, mai shekaru 34, Mista Eazi, ɗan asalin Nijeriya ne wanda ya samu lambar yabo ta fasaha a Nijeriya.

Ma'auratan sun yi bikin aurensu ne a wani coci da ke babban birnin ƙasar Iceland a ranar 8 ga Agustan 2025, amma ba a fitar da bidiyon shagalin bikin ba sai a kwanan nan.

Hakan ya nuna yadda aka kiyaye tare da sanya tsaro a ɗaurin auren.

A cewar mahaifin Temi, mutum 100 ne kawai aka gayyata.

Bayan hamshakin attajirin Afrika, Aliko Dangote, daya daga cikin hamshakan attajirai a cikin baƙin da suka samu halartar bikin akwai ɗan Nijeriya Abdulsamad Rabiu, wanda yana cikin attajirai 10 na nahiyar.

‘Dacewa da juna’

Bikin na Iceland shi ne shagalin taron bikin na uku da aka gudanar na Amarya Temi da Angonta Mista Eazi, wanda ainihin sunansa Oluwatosin Oluwole Ajibade.

A baya dai, sun yi bikin al’ada na auren a Monaco a ranar 9 ga Mayun 2025, sannan aka yi ɗaurin aure na gargajiya a gidan Femi Otedola da ke Dubai a ranar 5 ga Yuli.

Otedola ya ce ‘yarsa wadda ‘yar wasan kwaikwayo ce kuma mai tallar kayan ƙawa ta gabatar masa da Mista Eazi a shekarar 2017, kuma tun daga lokacin yake da yakinin mawakin zai zama miji na gari ga Temi.

"Temi ina yi miki fatan alkhairi a cikin dukkan al'amuran da ki ka sa gaba, kin samu miji mai albarka, ya fito daga gidan mutunci, abu daya (wanda zan ba ki shawara Temi shi ne, ki yarda da son mijinki, kin ji?

“Mijinki ne, shugabanki ne, babu sauran 'daddy, oh', na lura da su duka biyun, ba na son ki kira ni daddy, oh', wani abu da na lura da ku shi ne, tabbas kuna soyayya da juna, kuma kuna son juna,’’ in ji Otedola.

"Temi ƴar kasuwa ce, shi ma Tosin ɗan kasuwa ne. Don haka, kun dace da juna. Wannan (haɗi) ne daga Allah. Kai kuma Tosin, za ka je wurare da dama. Na ga ƙwarewar kasuwancinka," in ji shi.

Dangote ya taya su murna sosai

Ma’auratan sun samu shawarar uba inda y ce "Ka ci gaba da ƙaunar Temi. Idan kuna da matsaloli... ku ajiye su a tsakaninku kawai. Ka da ku kira wani na uku a tsakani balle ku shaida masa wannan matsala', Allah zai albarkace ku kuma ya albarkaci aurenku."

A nasa bangaren, hamshakin attajirin Afirka Aliko Dangote ya bayyana farin cikinsa ga ma’auratan tare da yi musu fatan alkhairi, kuma ya yi matukar mamaki tare da jin dadin sanin Mista Eazi yana yin kasuwanci a ƙasashen Afirka 18.

"Hakika na ji dadi sosai a yau. Nasan cewa Femi shi ne wanda ya fi kowa farin ciki a doron ƙasa a yau saboda ganin ranar da Temi ta auri Tosin. Kuma ina ganin Tosin ‘yarmu ta yi sa'ar samun miji irinka; mai nutsuwa.

A gaskiya ban taba sanin wani mawaƙi ɗan kasuwa, mai nutsuwa, mai aminci irinka ba. Don haka sai mu ce Allah ya saka maka," in ji Dangote.