Sabon ce-ce-ku-cen da ya ɓarke tsakanin Atiku Abubakar da Fadar Shugaban Nijeriya
NIJERIYA
3 minti karatu
Sabon ce-ce-ku-cen da ya ɓarke tsakanin Atiku Abubakar da Fadar Shugaban NijeriyaA yayin da Atiku ya ce babu wata alama da ke nuna cewa Shugaba Tinubu zai iya magance matsalar yunwa da talauci da suka addabi al’ummar ƙasar, Fadar Shugaban Kasar ta ce kalaman nasa ba su da ƙima.
Sabon ce-ce-ku-cen da ya ɓarke tsakanin Atiku Abubakar da Fadar Shugaban Nijeriya / TRT Afrika Hausa
3 awanni baya

Wani sabon ce-ce-ku-ce ya barke tsakanin tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar da Fadar Shugaban Ƙasar Bola Tinubu.

Atiku Abubakar, wanda daya ne daga cikin jagororin ’yan adawa a kasar, ya ce shekara biyu bayan Shugaba Bola Tinubu ya hau karagar mulki a kasar, babu wata alama da ke nuna cewa zai iya magance matsalar yunwa da talauci, wadanda suka addabi al’ummar Nijeriya.

Mai Magana da Yawun Shugaban Nijeriya, Bayo Onanuga ya yi watsi da kalaman na dan takarar shugabanci kasa a zaben shekarar 2023, inda ya bayyana su da kalamai marasa ƙima.

Mr Onanuga ya ce, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar da mutanen da ke tare da shi idonsu ya rufe dangane da cigaban da aka samu a kasar.

Atiku Abubakar ya ce, halin matsin rayuwa da ’yan kasar suke ciki abu ne da ba za a lamunta ba, kuma ya yi gargadin cewa matsananciyar yunwa da kunci suna cikin dalilan da suke jawo juyin juya hali a kasashen duniya.

A martaninsa, mai magana da yawun Shugaban Ƙasar ya ce babban kuskure ne yadda Atiku ya ce halin yunwa da ake ciki a Nijeriya ya yi kama da matsanancin halin da aka shiga a shekarar 1789, lokacin Juyin Juya Halin Faransa, da kuma Juyin Juya Halin Bolshevik wanda aka yi a kasar Rasha a shekarar 1917.

Mista Onanuga ya fada a shafinsa na X cewa, ’yan kasar suna alfahari da cigaban da aka samu karkashin gwamnatin Tinubu, kuma ya ce kalaman Atikun suna nuna yadda bai fahimci hakikanin abin da ke faruwa a zahiri ba a kasar.

Sannan Mista Onanuga ya kara da cewa, alkaluman da Hukumar Kididdiga ta Kasar (NBS) ta fitar sun nuna cewa a watan Agustan da ya gabata an samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki a kasar, wanda shi ne wata na biyar a jere da ake samun hakan saukin tsadar kayayyaki.

Kazalika ya ce lokacin da Tinubu ya hau mulki shekara biyu da suka wuce, akwai dala biliyan 32 a asusun ajiyar kuɗaɗen ƙetare na Nijeriya, amma yanzu abin da ke asusun ya kai dala biliyan 42.

Kuma ya ce gwamnatin Tinubu ta biya basussuka da suka kai dala biliyan bakwai ciki har da dala miliyan 800 da kamfanonin jiragen sama na ƙetare suke bi bashi.

Mai magana da yawun shugaban ya kuma ce yawancin matsalolin da kasar take fama da su sun samo asali ne daga kurakurai ta fuskar tattalin arziki da gwamnatin PDP ta tafka, wanda a cewar Onanuga, Atiku ya rike mukamin Mataimakin Shugaban Ƙasar a lokacin.

Mun tuntubi Dokta Baffa Kabiru Gwadabe, wanda ke koyarwa a fannin tattalin arziki a Jami’ar Bayero ta Kano don yin sharhi kan wannan cacar baki.

Dr Gwadabe ya fada wa TRT Afrika cewa, gaskiya ne an samu cigaba ta fuskar tattalin arziki a Nijeriya karkashin gwamnatin Bola Tinubu, musamman a watanni shida na farkon wannan shekarar.

Sannan masanin ya ce, ta fuskar hauhawar farashin kayayyaki nan ma an samu sauki bayan wasu matakai da gwamnatin kasar ta dauka.

Haka nan, hatta darajar kudin kasar naira a yanzu ya fara daidaita, wanda shekaru biyu da suka gabata ba haka abin yake ba.

Ko da yake malamin jami’ar ya ce akwai wasu bangarorin tattalin arziki da gwamnati ba ta yin abin da ya kamata, har ya bayar da misalin yadda gwamnatin Tinubu take ci gaba da ciyo bashi daga ƙasashen ƙetare.